Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar Nijeriya da su sake ba wa gwamnatinsa wata sabuwar dama domin kammala manyan shirye-shirye da sauye-sauyen tattalin arziƙin da ta fara aiwatarwa a ƙasar.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, wanda ya wakilci shugaban ƙasar, ya bayyana cewa gwamnatin na ƙoƙarin gyara tarin kurakurai da damarmakin da gwamnatocin baya suka yi asararsu. Ya ce: “Saƙona ga ƴan ƙasa a madadin Shugaban Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattawa da mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa shi ne kada al’umma su fidda rai, domin zaman lafiya da ci gaba na dawowa a ƙasar nan.”
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata addu’ar Juma’a ta musamman da aka gudanar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, a matsayin ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da Nijeriya ta samu ƴancin kai.
Da yake tsokaci kan bikin ƴancin kan, Abbas ya bayyana cewa cika shekaru 66 ya nuna cewa Nijeriya ta kai wani mataki, inda ya ƙara da cewa duk da an fuskanci ƙalubale daban-daban a tafiyar da aka yi a baya, yanzu haka ƙasar na kan turbar samun ci gaba.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa akwai haske a gaba, yana mai cewa ƴan ƙasa sun riga sun gama sadaukarwar da ake buƙata domin mayar da ƙasar muhimmiya, don haka ya kamata a bai wa gwamnatin ƙarin dama domin ta kammala kyakkyawan aikin da ta fara.














