Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargaɗi masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da su gaggauta ajiye aikinsu idan har suna jin cewa ba a yi musu adalci ba ko kuma ba sa samun abin da suke tsammani a fannin rabon kuɗi ko tagomashin ofis.
Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, da sauran shugabannin hukumomi a gwamnatin jihar, inda ya jaddada cewa shiga aikin gwamnati wata kafa ce ta sadaukarwa domin ceto da kuma sake gina Jihar Zamfara daga ƙalubalen tsaro da ta faɗa ciki, ba wai hanyar neman tara abin duniya ba.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta rungumi tsarin tsantseni da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen al’umma, don haka duk wani jami’in gwamnati da ke tsammanin samun kuɗi ta hanyoyin da ba su dace ba ko kuma yake ganin an danne masa haƙƙi, ya fi dacewa ya yi murabus cikin lumana domin bai wa waɗanda ke da kishin jihar damar yin aiki.
Haka kuma, Gwamnan ya buƙaci waɗanda suka zaɓi ci gaba da aiki a gwamnatin da su maida hankali wajen aiwatar da manufofin kawo sauyi, inganta rayuwar al’ummar karkara, da kuma tallafa wa ƙoƙarin da ake yi na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada aniyarsa ta sanya muradun talakawan Jihar Zamfara a gaba da duk wata masalaha ta siyasa ko ta ɗaiɗaikun mutane, yana mai gargaɗin cewa ba zai amince da duk wani aiki na zagon ƙasa ko nuna halin ko-in-kula da zai kawo cikas ga tafiyar da ayyukan gwamnatin ba.














