Kwamitin Sulhu na MDD ya amince da kudurin tsawaita takunkumansa game da yankin Darfur na Sudan, na gajeren lokaci.Kudurin mai lamba 2828 wanda ya samu amincewar dukkan mambobi 15 na kwamitin a jiya Juma’a, ya tsawaita takunkuman ciki har da na sayarwa da samar da makamai da matakan hana tafiye-tafiye da na haramta amfani da kadarori, har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba.
Mukaddashin mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun lei, ya yi bayani game da kuri’ar da aka kada wa kudurin, yana mai gargadi game da fadada bangarorin da takunkuman suka shafa. Ya ce bisa la’akari da bambancin da ke akwai tsakanin mambobin kwamitin, Amurka da ta tsara kudurin, ta bayar da shawarar tsawaita matakan takunkuman na gajeren lokaci da wata daya a yankin Darfur na Sudan, wanda zai ba mambobin lokacin tuntuba. Ya ce kasar Sin ba ta da ja kan hakan kuma ta kada kuri’ar amincewa da shi.
Haka kuma, ya ce kasar Sin ta kasance har kullum mai tabbatar da adalci da gaskiya da shigar da kowa cikin tsara kuduri, tare da kauce wa tilasta aiwatar da kuduri mai sarkakiya.Bugu da kari, Sun Lei ya ce Sin na fatan bayan tuntubar juna da za a yi, dukkan bangarori za su kara karfafa hadin gwiwa da tuntubar juna, tare da la’akari da korafe-korafen dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da cimma matsaya nan ba da dadewa ba, tare da taka rawar gani wajen ingiza tsagaita wuta da dakatar da yaki a Sudan da kuma tabbatar da hadin kai da martabar kasar ta Sudan. (Fa’iza Mustapha)













