Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan India Narendra Modi a birnin New Delhi, a gefen taron kungiyar kasashen BRICS.Xi Jinping, ya ce Sin da India za su iya daukar darasi daga karfin juna da samun ci gaba na bai daya.
Kuma ya kamata Sin da India su goyi bayan samar da tsarin duniya mai adalci da tsari da rarrabuwar iko tsakanin kasashe. Bugu da kari, ya ce Sin na daukar dangantakarta da India daga mai muhimmanci zuwa mai dorewa.
Sannan ya bukaci kasashen biyu su hada hannu wajen samar da ingantaccen ci gaba a fannin raya hadin gwiwar kungiyar kasashen BRICS. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT













