ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwankwaso Ba Shi Da Niyyar Ficewa Daga NDC – Kwankwasiyya

by Sadiq
3 months ago

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin ficewa daga jam’iyyar NDC.

Rahotannin sun biyo bayan labarin cewa jam’iyyar ta maye gurbin wasu ‘yan takarar da ƙungiyar ta gabatar a Jihar Kano.

Da yake magana kan lamarin, kakakin Kwankwasiyya, Dokta Habib Sale, ya ce babu wata tattaunawa ko shawara da aka yanke kan batun ficewar Kwankwaso daga jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana rahotannin a matsayin jita-jita da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta.

“Shugabanmu bai taɓa tattaunawa da kowa kan ficewa daga jam’iyyar ba. Mu ma mun ga labarin ne kamar kowa,” in ji Sale.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

Ya kuma bayyana cewa an zaɓi ‘yan takarar da Kwankwasiyya ta goyi baya ne ta hanyar zaɓen fidda-gwani da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, kuma an bi dukkanin matakai ba tare da wata matsala ba a lokacin.

A cewarsa, an miƙa jerin sunayen ‘yan takara bayan kammala zaɓen, kuma duk wani mataki da za a ɗauka yanzu yana hannun jam’iyya bisa ƙa’idojinta.

Wannan bayani ya biyo bayan rahotannin da ke cewa NDC ta sauya wasu ‘yan takarar da Kwankwasiyya ta gabatar a Kano, sakamakon saɓani kan yarjejeniyar raba muƙamai tsakanin ɓangarorin biyu.

Rahoton ya nuna cewa an ware kashi 60 cikin 100 na muƙamai ga Kwankwasiyya, yayin da kashi 40 cikin 100 kuma aka bai wa ɓangaren jam’iyyar na asali.

Duk da wannan rikici, Kwankwasiyya na ci gaba da cewa ba a yanke wani hukunci ba kan makomar dangantakarta da jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
Sin Da Afrika Ta Kudu Na Ci Gaba Da Zurfafa Hadin Gwiwa A Bangaren Soji

Sin Da Afrika Ta Kudu Na Ci Gaba Da Zurfafa Hadin Gwiwa A Bangaren Soji

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.