Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Jam’iyyar APC mai mulki da kulla makarkashiyar maguɗi da sauya sakamakon babban zaɓen 2027, sakamakon fargabar da jam’iyyar ke ciki kan ƙaruwar farin jinin ƴan takarar adawa.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a cikin shirin Politics Today, Kwankwaso ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri daga mutanen da ke kusa da jiga-jigan APC, inda ya ce ƴan jam’iyya mai mulkin na bugun kirji da cewa ko da ƙuri’u 1,000 kacal suka samu a akwati, za su rubuta sakamakon da kansu.
Sai dai yayin da aka tambaye shi ko yana da kwararan hujjoji a rubuce kan wannan iƙirari, Kwankwaso ya amsa da cewa ba shi da hujjoji kai-tsaye, amma labarin na fitowa ne daga mutanen da ke kusa da manyan jiga-jigan jam’iyyar ta APC.
Kwankwaso ya ƙara da cewa fargabar da ta dabaibaye jam’iyya mai mulki ta samo asali ne daga gagarumin karɓuwar da haɗakar ƴan takarar adawa ta samu a sassan ƙasar, inda ya bayyana cewa goyon bayan da Peter Obi ke da shi a yankin Kudu da kuma ɗimbin magoya bayan Ƙungiyar Kwankwasiyya a yankin Arewa sun samar da wata ƙaƙƙarfar rundunar siyasa da ke barazana ga ci gaba da zaman APC a kan mulki.
A ƙarshe, tsohon gwamnan ya caccaki gwamnonin da ke mara wa shirin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a maimakon mayar da hankali kan matsalolin jihohinsu, yana mai gargaɗin cewa a ranar zaɓe APC za ta fahimci babban kuskuren da ta tafka. Ya jaddada cewa mawuyacin halin da ƴan ƙasa suka tsinci kansu a ciki musamman matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya da tsananin talauci da tsadar rayuwa da gwamnati ta kasa shawo kansu, su ne ainihin abubuwan da za su sa ƴan ƙasa su yi watsi da jam’iyya mai mulki a akwatin zaɓe.














