Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta gayyaci Malam Dahiru Abubakar, wanda aka fi sani da Danmalam ko Jejiwe, domin jin ƙarin bayani kan zargin cire shi daga limancin wani masallaci saboda tallata takarar Shugaba Bola Tinubu.
Gayyatar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da rahotannin kafafen yaɗa labarai suka haifar, inda aka bayyana cewa an cire malamin daga limancin masallacin da ke Madina Quarters, Bauchi, saboda siyasa.
A yayin ganawarsa da hukumar, malamin ya yi zargin cewa wasu kafafen yaɗa labarai sun karkatar da kalamansa, yana mai cewa ƙaramin masallaci ne da ba ya wuce mutane bakwai ke gudanar da sallah a cikinsa, ba babban masallacin Juma’a ba ne.
Ya tabbatar da cewa waɗannan mutane ne suka cire shi daga limanci, amma ya ce sun riga sun sasanta tsakaninsu kan batun.
Malam Danmalam ya nemi afuwar waɗanda lamarin ya ɓata wa rai, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa gabatar da kalamansa yadda ya faɗe su.
Hukumar, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Hisba, Malam Muhammad Muhammad Bununu, ta ba shi shawarwari kan kauce wa haɗa harkokin addini da siyasa ta hanyoyin da ba su dace ba.
Sai dai malamin ya jaddada cewa har yanzu yana goyon bayan Shugaba Tinubu da ƙoƙarin tallata takararsa.














