Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a, Imaan Sulaiman Ibrahim, ta bayyana cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, na tallafa wa mata ne saboda tausayi da jinƙai.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin rabon kayayyakin tallafi a gidan gwamnatin Jihar Nasarawa da ke Lafia, inda ta ce shirin zai amfani mata tsakanin 1,000 zuwa 3,000.
Ta ce tallafin ya haɗa da rabon rumfunan kasuwanci da kuma ba wa mata 100 zuwa 200 jarin naira 100,000 kowacce domin bunƙasa sana’o’insu.
Imaan ta ƙara da cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa na ziyartar asibitoci domin tallafa wa mata masu jego, tare da kula da halin da mata ’yan kasuwa ke ciki.
Ta ce bayan kammala shirin a Nasarawa, tawagar za ta kai tallafin jihohin Ekiti da Oyo, sannan ta wuce Fatakwal.
Ministar ta kuma bayyana kwarin gwiwar cewa ’yan Nijeriya za su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu, tana mai cewa idan ya samu wa’adi na biyu, shirin tallafa wa mata zai inganta.
Da take martani kan zargin cewa tallafin na da alaƙa da siyasa, ta ce ayyukan da Oluremi Tinubu ta gudanar cikin shekaru uku sun nuna jajircewarta wajen taimaka wa mata.













