ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mahangar Al’ummun Afirka Dangane Da Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanya Tsakanin Al’ummun Sin Da Na Afirka

by Sulaiman and CGTN Hausa
8 months ago
Afirka

Bayan kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka a shekarar nan ta 2026, masharhanta  da dama musamman daga kasashen Afirka, na ganin an dauki wata hanya ta kara raya cudanya tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda hakan ke nuni ga fadada alakar sassan biyu daga samar da ababen more rayuwa, da bunkasa hada-hadar cinikayya zuwa zurfafa sada zumunta, da raya zamantakewar al’ummun sassan biyu.

Ko shakka babu, bunkasa musaya tsakanin al’ummun Sin da na kasashen Afirka zai yaukaka amincewa da fahimtar juna, da raba kwarewa a fannin sanin makamar aiki musamman ga al’ummun kasashen Afirka masu tasowa. Karkashin wannan manufa, dalibai, da matasa, da kwararru da masu sana’o’i, da masu bincike, da ma’aikatan kafofin watsa labarai za su samu zarafin cudanya kai tsaye, tare da gane yadda bangarorin biyu ke gudanar da manufofin raya ci gaban al’umma. Kuma sannu a hankali, za su kai ga bude sabbin babuka na hadin gwiwa mai dorewa.

A gani na wani abu da ya bambanta sabuwar manufar nan ta raya musayar al’adu da cudanya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka, da manufofi makamantanta na baya, shi ne dora karin muhimmanci kan ci gaban al’ummu, da cudanyar jama’a a matakin farko. Wannan kari ne kan manufofin baya, na samar da ababen more rayuwa, irinsu hanyoyin mota, da layukan dogo, da hakar ma’adanai da hada-hadar kudade da dai sauransu.

ADVERTISEMENT

Kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka a shekarar nan ta 2026, ya zamo jigon mayar da karin matasan nahiyar Afirka masu dogaro da kai, kana za a kai ga raya al’adu, da ilimi da kafafen watsa labarai. Har ila yau, karkashin hakan an tsara aiwatar da ayyuka kusan 600, matakin dake nuni ga shirin wanzar da aniyar raya zamantakewar al’ummun Afirka cikin dogon lokaci, wanda hakan na da matukar muhimmanci ga cimma nasarar bunkasa cinikayya, da zuba jari, da hadin gwiwar samun ci gaban bai daya na shekaru masu yawa a nan gaba.

A kasashen Afirka, wannan manufa za ta samar da muhimman damammaki na raya sanin makamar aiki, musamman a gabar da kasashen nahiyar ke ta kokarin fadada hanyoyin raya tattalin arzikinsu, da neman hanyoyin magance kalubalen kamfar guraben ayyukan yi tsakanin matasa.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Ko shakka babu wannan manufa ta musayar al’adu da cudanya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka za ta taimaka kwarai wajen gina kwarewar ayyuka, da horar da matasa, da musayar ilimi a muhimman sassa. A daya bangaren kasashen Afirka, za su iya yin koyi daga kwarewar Sin a fagen bunkasa masana’antu, da fasahohin dijital, da yawon bude ido, da bunkasa kananan sana’o’i da dai sauransu.

Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Har Lahira A Neja

Ɗalibin Jami'a Ya Hallaka Kansa Har Lahira A Neja

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.