ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mahangar Wakiliya Mai Fasahar Wasan Kwaikwayo Game Da Dimokuradiyyar Dake Shafar Kowa Da Kowa A Nan Kasar Sin

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
{"ARInfo":{"IsUseAR":false},"Version":"1.0.0","MakeupInfo":{"IsUseMakeup":false},"FaceliftInfo":{"IsChangeEyeLift":false,"IsChangeFacelift":false,"IsChangePostureLift":false,"IsChangeNose":false,"IsChangeFaceChin":false,"IsChangeMouth":false,"IsChangeThinFace":false},"BeautyInfo":{"SwitchMedicatedAcne":false,"IsAIBeauty":false,"IsBrightEyes":false,"IsSharpen":false,"IsOldBeauty":false,"IsReduceBlackEyes":false},"HandlerInfo":{"AppName":2},"FilterInfo":{"IsUseFilter":false}}

A lokacin tarukan majalissun NPC da CPPCC na kasar Sin na shekara ta 2025, wakiliya a majalisar wakilan jama’a ta kasar Sin wato NPC, kana shugabar gidan wasan kwaikwayon Min na Fujian, Zhou Hong, ta bayar da wata shawara, wadda ta sa tsohon wasan kwaikwayo na Min ya samu sabon kuzari.

Zhou Hong wadda ta lashe lambar yabo ta wasan kwaikwayo ta Plum Performance ta Sin, ta kwashe shekaru tana taka rawar gani a dandalin wasan kwaikwayo, inda ta mayar da hankali kan abubuwan da suka hana samun ci gaba a fannin, kamarsu rashin isassun masu gadon al’adun gargajiya na wasan kwaikwayo, da rashin ingantaccen tsarin horar da ‘yan wasa matasa… Wadannan matsaloli, tana ganinsu da ido, tana kuma damuwa a zuciya.

Domin sauke nauyin dake wuyanta a matsayin wakiliyar majalissar NPC, a shekarar 2025, yayin taron NPC, Zhou Hong ta bayar da shawarwarin karfafa aikin horar da masu gadon al’adun gargajiya, da kuma kafa cibiyoyin musayar al’adun wasan kwaikwayo na Fujian da Taiwan na musamman. Bayan gabatar da shawarwarin, ma’aikatar al’adu da yawon bude ido da sauran hukumomin da abin ya shafa sun dora musu da muhimmanci sosai, sun kuma sha tattaunawa da ita, kana sun karbi shawarwarinta.

ADVERTISEMENT

Hakika yadda aka aiwatar da shawarwarin cikin matukar sauri ya ba Zhou Hong mamaki. An shigar da kariya da gadon wasan kwaikwayo na Min cikin ayyukan kare al’adu na lardunan kasar Sin da dama, kuma an inganta tsarin horar da ‘yan wasa matasa. Gidajen wasan kwaikwayo sun fara hada kai da makarantu kusan 20 a duk shekara, kuma yara suna kara fahimtar fasahohin wannan wasan kwaikwayo. “Tabbatar da dimokuradiyyar dake shafar kowa da kowa ba maganar banza ba ce, ana iya ganin yadda ake aiwatar da tsarin a tattaunawar da ake yi, da yadda ake wasu aikace-aikace bisa shawarwarin da aka gabatar, kuma a kowane mataki na aiwatar da manufofin da aka tsara.” Maganar Zhou Hong ta bayyana ma’anar aikin wakilan majalisar NPC.

Labarin Zhou Hong, misali ne na aikin tabbatar da dimokuradiyyar dake shafar kowa da kowa: gwamnati za ta saurara da amsar shawarwarin wakilai, za ta kuma aiwatar da ayyuka bisa shawarwarin a iyakacin kokari. Jama’a suna da hanyoyin bayyana ra’ayoyinsu, kuma gwamnatin za ta kula da bukatunsu. Wannan shi ne ma’ana da fifikon dimokuradiyya irin ta Sin.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14 (2021-2025), yawan shawarwarin wakilan majalisar NPC da majalisar gudanarwa ta Sin ta karba ya kai 42879, kan adadin shawarwarin da majalisar CPPCC ta gabatar wadanda aka lura da su ya kai 25,789, kuma an dauki matakai bisa wadannan shawarwari cikin lokaci.

Za a gudanar da tarukan shekara-shekara na majalissun NPC da CPPCC a kwanaki masu zuwa. A wannan karo, Zhou Hong tana da sabon tunani. Tana shirin bayar da shawarwari kan kara inganta musayar al’adun wasan kwaikwayo tsakanin babban yankin Sin da yankin Taiwan na kasar, da kuma inganta hadin gwiwarsu a fannonin al’adu da yawon bude ido.

An yi imanin cewa a wannan shekarar da muke ciki, wadda ta kasance shekara ta farko ta aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, za a samu karin wakilai da za su gabatar da shawarwari a tarukan majalissun NPC da CPPCC, wadanda za su samar da gudunmowa a yunkurin aiwatar da shirin raya kasar ta Sin. (Mai zane da rubutu: MINA)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 2

Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 14

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.