Majalisar Koli ta Shari’a a Nijeriya (SCSN) ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sake duba ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, tana mai gargadin cewa matakan da aka dauka, akan iya ganinsu a matsayin na son rai ko kuma na siyasa wanda hakan ka iya rage amincewar jama’a ga cibiyoyin dimokuradiyyar Nijeriya.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren majalisar, Nafi’u Baba-Ahmad, ya sanya wa hannu ranar Talata.
SCSN ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa ana bin ka’idojin shari’a yadda ya kamata wajen tafiyar da shari’ar El-Rufa’i, tana mai jaddada cewa dole ne a yi amfani da doka daidai ga dukkan ’yan kasa, ba tare da la’akari da matsayinsu, alakar siyasa ko ra’ayinsu na kashin kansu ba.
Majalisar ta ce tana nan kan matsayinta na tabbatar da adalci, gaskiya da bin doka, tana mai cewa kowane ɗan Nijeriya yana da hakkin samun muhimman hakkokinsa na dan Adam, kuma doka ta dauke shi a matsayin marar laifi har sai kotun da ta dace ta tabbatar da laifinsa.
Majalisar ta bayyana cewa ba ta goyon bayan aikata laifuka ko kuma kare masu aikata su, amma ta jaddada cewa neman adalci shi ma dole ne ya kasance bisa ka’idojin shari’a da kundin tsarin mulki da aka tanada.














