ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Wakilai Ta Fara Yunƙurin Gyaran Dokokin Soja

by Sulaiman
3 months ago

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta fara nazarin wasu muhimman ƙudurorin dokoki da suka shafi harkokin tsaro, da nufin ƙarfafa tsarin rundunonin sojin Nijeriya, inganta walwalar jami’an soja da tsofaffin sojoji, da kuma ƙara wa rundunar ƙarfi wajen tunkarar sabbin barazanar tsaro.

Da yake jawabi a taron sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu da Kwamitin Tsaro na Majalisar ya shirya a Abuja, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce an tsara ƙudurorin ne domin magance sauye-sauyen ƙalubalen tsaro da kuma gina rundunar soja mai ƙarfi da tasiri.

Ya bayyana cewa ƙudurorin sun yi daidai da manufofin Majalisar Wakilai ta 10, kuma suna nuna ƙudirin ƴan majalisa na sake fasalin bangaren tsaron ƙasa.Abbas ya ce sabbin barazanar tsaro kamar fashin teku a yankin Tekun Guinea, yaƙin da damfara a Intanet, da haɗin gwiwar masu aikata manyan laifuka da ƴan ta’adda, sun ƙara nuna buƙatar yin gyare-gyare masu zurfi a fannin tsaro.Daga cikin manyan ƙudurorin da ake dubawa akwai: Dokar Shirin Gonaki da Kiwon Dabbobi na Rundunar Soji, wadda ke da nufin haɗa tsaron abinci da ayyukan soja, musamman a yankunan da ake fama da rikice-rikice.

ADVERTISEMENT

Dokar Wakilcin Mata a Rundunar Soji, domin ƙarfafa ba mata damar shiga aikin soja da samun wakilci mai kyau.Dokar Rundunar Sojin Nijeriya, wadda za ta soke tare da maye gurbin tsohuwar Dokar Rundunar Soji domin dacewa da yanayin zamani.

Dokar Ƙungiyar Tsofaffin Sojojin Nijeriya, da ke neman inganta walwala da jin daɗin tsofaffin jami’an soja.Kakakin Majalisar ya buƙaci masu ruwa da tsaki, ciki har da jami’an soja masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, ƙungiyoyin farar hula, masu fafutukar kare haƙƙin mata, lauyoyi da sauran jama’a da su bayar da gudunmawarsu a wannan tsari na doka.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Tun da farko, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Babajimi Benson, ya bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ga ƴan ƙasa da masu ruwa da tsaki su bayar da gudunmawa wajen tsara dokokin da za su ƙarfafa tsarin tsaro da kariyar Nijeriya.

Ya ce ƙudurorin sun shafi muhimman fannoni kamar ilimin soja da horar da jami’ai, inganta haɗin gwiwar ayyukan tsaro, kiwon lafiya, bincike da dabarun soja, walwalar tsofaffin sojoji, gyaran tsarin gudanarwa, tsaron abinci da kuma ƙarfafa shigar mata a rundunar soji.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.