ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ɗiyata Tilo Ta Mutu A Wata Makarantar Sakandire A Kano – Mahaifiya

by Abubakar Sulaiman
3 months ago

Iyalan Marigayiya Maimuna Sani (Nihal), ɗaliba mai shekaru 14 a aji biyu a karamar sakandare (JSS2) sashin makarantar kwana ta St. Louis da ke Kano, sun nemi a yi musu adalci bayan rasuwarta cikin yanayi mai cike da ruɗani da ake ta cece-kuce kan makarantar.

Iyalan yarinyar sun ce an ba su bayanai mabambanta kan musabbabin mutuwar Nihal. Yayin da makarantar ta ce ta rasu ne sakamakon tashin ciwon cutar asma, wasu bayanai sun nuna cewa an hukunta ta ne saboda jinkirin zuwa masallaci, inda ake zargin manyan ɗalibai mata sun yi mata bulala tare da tilasta mata yin durƙushe na tsawon lokaci kafin ta faɗi ta suma.

Mahaifiyarta, Nusaiba Rabiu Dan Sheriff, ta ce an kira iyalinsu zuwa asibiti inda aka tabbatar musu da mutuwar yarinyar. Ta bayyana cewa ma’aikatan asibitin sun tambaye su ko Nihal na fama da cutar asma, lamarin da ya ƙara jefa su cikin shakku. Ta kuma ce ta lura da wasu alamomi a jikin gawar ɗiyarta da suka sa ta fara tambayar ko an ɓoye mata wani abu game da abin da ya faru.

ADVERTISEMENT

Ta ce tana da yaƙinin akwai wasu bayanai da har yanzu ba a bayyana ba, saboda haka ta buƙaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a mutuwar yarinyar.

Da aka tuntuɓi shugabar makarantar, Reverend Sister Christiana Diyab, ta ce ba za ta yi magana kan lamarin ba a yanzu saboda yana hannun ‘yansanda. A nata ɓangaren, Rundunar ‘Yansandan Kano ta tabbatar da kafa kwamitin bincike na musamman bayan karɓar ƙorafi daga iyalan marigayiyar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Daily Trust ta rawaito cewa, rundunar ta ce ta gayyaci malamai uku, manyan ɗalibai mata uku da wasu shaidu biyu domin bayar da bayani, yayin da ake ci gaba da gwaje-gwajen likitanci da na kimiyyar bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar Nihal.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Manzon Allah

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.