ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Sin Ta Soke Harajin Kwastam Ga Kasashen Afirka Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Bangarorin Biyu

by Sulaiman
4 months ago
Sin

Shekarar bana ita ce ta cika shekaru 70 da fara kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma shekara ta farko ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15. A cikin wannan shekara ta musamman, wata yarjejeniya game da harajin kwastam ta zo a kan lokaci kamar yadda aka zata.

Daga yau Juma’a, wato 1 ga watan Mayu, Sin ta fara soke harajin kwastam na tsawon shekaru biyu ga kasashe 20 na Afirka da ke da dangantakar diflomasiyya da ita, wadanda ba su cikin kasashe mafi karancin ci gaba. Ta haka ne za a cimma burin soke harajin kwastam ga dukkannin kasashe 53 na Afirka masu dangantaka da Sin.

To, mene ne manufar ta soke harajin kwastam za ta kawo wa Afirka?Da farko, wannan mataki yana ba wa Afirka kariya don fuskantar kalubale da hadurra.

ADVERTISEMENT

A halin yanzu, ana kara samun tabarbarewar yanayin siyasa a duk duniya, yayin da ra’ayin ba da kariyar ciniki da na bangaranci ke karuwa.

Saboda haka, kasashen Afirka suna bukatar gaggauta fadada fitar da kayayyaki zuwa ketare da jawo jari daga waje, domin kawar da matsalolin da ke dakile ci gabansu.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Yadda kasar Sin ta soke harajin kwastam ga Afirka a dukkan fannoni ba tare da gindaya wani sharadi na siyasa ba, babu shakka yana ba wa kayayyakin Afirka damar shiga kasuwa mafi girma, kuma yana karfafa gwiwar kasashen Afirka wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikinsu.

Baya ga haka kuma, manufar za ta gaggauta ci gaban kasashen Afirka, duba da cewa hakan zai jawo karin jarin waje zuwa Afirka, baya ga fasahohi da ma kwarewar gudanarwa, wanda hakan zai taimaka wajen sarrafa kayayyaki a kasashen Afirka, sannan a fitar da su zuwa Sin.

Hakan kuma zai taimaka wa Afirka wajen bunkasa masana’antu da zamanantar da aikin gona, ta yadda Afirka za ta rike ragamar ci gaba a hannunta sosai.

Wannan “takardar izini” ta soke harajin kwastam, ba wai kawai ta bude sabon shafi na hadin gwiwar Sin da Afirka ba ne, har ma ta kara wa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa da kuma karfin kuzari, sannan ta sa al’ummar duniya sun fahimci cewa, bude kofa, da hakuri da juna, da samun ci gaba tare, su ne hanya madaidaiciya. (Bilkisu Xin)

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

Shugaban ADC Tsagin Nafiu Bala Ya Fice Daga Jam’iyyar, Ana Hasashen Zai Koma APC

LABARAI MASU NASABA

Sin

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.