ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Soke Haraji Ta Sin: Kyakkyawan Misali Da Ke Adawa Da Kariyar Cinikayya

by Sulaiman
3 weeks ago
default

default

An gudanar da wani taron kara wa juna sani game da manufar soke haraji ta kasar Sin ga kasashen Afrika 53 masu huldar diplomasiyya da ita, a birnin Abujan Nijeriya a karshen mako, wanda ya samu halartar jakadan Sin a Nijeriya da karamin ministan kula da cinikayya da sauran manyan jami’ai na kasar. Har kullum, idan masana suna zancen bunkasa tattalin arziki a Nijeriya, su kan yi jan hankali kan kasar ta yi hobbasa ta rika fitar da kayayyaki ketare domin bunkasa harkokin masana’antu a cikin gida da samar da aikin yi da karfafa tattalin arzikinta. Ba Nijeriya ba, kusan dukkan kasashen Afrika ne suke dogaro da shigar da kayayyaki maimakon fitar da su.

A ganina, manufar ta kasar Sin ta tabbatar da burin da aka dade ana son gani, watau kasashen nahiyar Afrika su zama masu sarrafa kayayyaki da albarkatun da suke da shi domin karfafa tattalin arzikinsu da dogaro da karfinsu da kyautata rayuwar jama’a. Wannan manufa ta farkar da kasashen Afrika da karfafa musu gwiwar cin ribar albarkatun da suke da shi yadda ya kamata, lamarin da zai bunkasa samar da aikin yi da ma kwarewa a kasashen.

Uwa uba, manufa ce da ke nuna burin kasar Sin na ganin kasashen Afrika sun zama masu tsayawa da kafafunsu maimakon masu jira a taimaka musu. Rahotanni sun ruwaito cewa, tun bayan fara aiwatar da manufar a ranar 1 ga watan Mayun bana, an samu habakar fitar da kayayyaki daga Nijeriya zuwa kasar Sin inda darajar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta kai dala biliyan 18. Kana yawan kayayyakin da ake fitarwa daga Nijeriya zuwa Sin ya karu da kaso 80 zuwa dala biliyan 2.3, inda karuwar da ake samu a kowane wata ya zarce kaso 40 a watan Mayu da Yuni. Irin wannan kyakkyawar dangantaka da Sin, ita ce ainihin hadin gwiwar da ya kamata a rika gani tsakanin kasashen duniya, inda za a rika samun moriyar juna da tallafawa marasa karfi ta yadda za su tsaya da kafafunsu, ba wai tallafi mai sharadi da zai mayar da su karkashin ikon wata kasa ba.

ADVERTISEMENT

Tasirin wannan manufa ba zai misaltu ba, domin idan kasashen Afrika suka yi amfani da ita yadda ya kamata, abu ne da zai kara inganta hadin kansu da dunkulewarsu guri guda musammam bisa la’akari da yarjejeniyar cinikayya cikin ’yanci ta Afrika da ke akwai a tsakaninsu.

Har ila yau, ta zama kyakkyawan misali dake adawa da kariyar cinikayya tare da bude kofar karfafa cinikayya mai adalci tsakanin kasa da kasa ba tare da gindaya sharudda ba, da kuma karfafa hadin kan kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Haraji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
Haraji

Babu Shugaban Da Ya Yi Wa Nijeriya Aiki Kamar Babangida - Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.