Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai murabus) murnar cika shekaru 85 da haihuwa, inda ya bayyana cewa babu wani shugaban da ya kawo ci gaba ko yin tasiri a Nijeriya kamarsa.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a madadinsa.
A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya siffanta Janar Babangida a matsayin jajirtaccen shugaba wanda mulkinsa na tsawon shekaru takwas ya bar tarihi marar gushewa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kuma fasalin ƙasar nan. Ya bayyana cewa tsohon shugaban ya faɗaɗa tattalin arzikin ƙasa, ya gina muhimman ayyukan more rayuwa masu ɗorewa, tare da kafa hukumomin da har yanzu suke ci gaba da amfanar da buƙatun ƙasa.
Shugaban ƙasar ya ci gaba da cewa, da ba don hangen nesa, da hikima, da kuma adalcin Janar Babangida ba, da yawa daga cikin jihohin da muke da su a Nijeriya a yau ba za su kasance ba. Ya jaddada cewa gudunmuwar da tsohon shugaban ya bayar wajen gina ƙasa za ta ci gaba da zama a rubuce babu gogewa a cikin kundin tarihin Nijeriya.
Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yaba wa IBB bisa yadda yake ci gaba da bayar da shawarwari masu amfani ga ci gaban ƙasa koda yake yana gudanar da rayuwar ritayarsa cikin kwanciyar hankali a gidansa na Minna Hilltop a Jihar Neja.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa tsohon shugaban albarka, da ba shi ƙoshin lafiya da ƙarin karfi, don ci gaba da kasancewa abin koyi ga matasa masu tasowa.













