ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamnan Zamfara Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro Bisa Ƙwato Ɗarurruwan Shanu

by Sulaiman and Hussein Yero
3 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi da jajircewarsu wajen yaƙi da ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Yabon na gwamnan ya biyo bayan nasarar da Sashen Daƙile Ayyukan Ta’addanci da Rikice-rikice, wato Violence Crime Response Unit – VCRU, na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ya samu na ƙwato shanu 329 da tumaki 175 daga hannun ’yan bindiga a dajin Gambanda da ke Ƙaramar Hukumar Gummi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce Gwamna Lawal ya bayyana cewa sabon ƙaimi da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ke nunawa wajen yaƙi da matsalar tsaro alama ce mai ƙarfafa gwiwa kuma abin yabawa.

ADVERTISEMENT

“Na yaba da ƙoƙarin dukkan jami’an tsaro da ke aiki a Jihar Zamfara, musamman Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, saboda juriyarsu, jarumtarsu da kuma sadaukarwarsu wajen ƙwato shanu 329, tumaki 175, makamai da alburusai daga hannun ’yan bindiga,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron sun fafata da ’yan bindigar tare da murƙushe su a dajin Gambanda da ke Ƙaramar Hukumar Gummi, lamarin da ya haifar da samun wannan gagarumar nasara.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Gwamnan ya bayyana cewa wannan nasara wata shaida ce ta irin sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi duk da ƙalubalen da suke fuskanta daga masu aikata laifuka, tare da nuna muhimmiyar rawar da rundunar ’yan sanda ke takawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Zamfara.Ya ce, nasarar ƙwato dabbobin da makamai daga hannun ’yan bindiga ta nuna ƙwarewa da jarumtaka, tare da nuna irin shugabancin da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmed Muhammad Bello, ke bayarwa.

A cewarsa, jagorancin kwamishinan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro da kuma ƙarfafa yaƙi da matsalar ’yan bindiga a jihar.Gwamna Lawal ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

Zamfara
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Zamfara
Hussein Yero
+ posts Bio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Kudirin Yaki da ‘Yan Ta’adda Ba Tare Da Sulhu Ba
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    ’Yan Bindiga Sun Sace Dattawan Zamfara 50 Yayin Taron Sulhu A Cikin Daji
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Ɗan Takarar Sanata A Zamfara Ya Koka Kan Yi Wa Rayuwarsa Barazana
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Abdulaziz Yari Ya Bukaci Limamai Su Ƙara Addu’a Kan Yaƙi Da Ƴan Bindiga A Zamfara

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
ADC Ta Sake Tabbatar Da Ibrahim Khalil A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano Na 2027

ADC Ta Sake Tabbatar Da Ibrahim Khalil A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano Na 2027

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.