Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘Yan Bindiga ba, kuma ba za ta mika wuya ga ‘yan ta’adda ba a Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Bala Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis.
A cewarsa, A yau Alhamis Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Karamar Hukumar Bungudu domin yin ta’aziyya ga iyalai da harin ‘yan bindiga ya shafa, da masarauta, da iyalan da suka rasa rayukan su sakamakon harin ‘yan bindiga da su aka kai kwanan nan.
Ziyarar ta fara ne a fadar Mai Martaba Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, inda Gwamna Lawal ya bayyana kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Ya ce: “Na zo ne domin nuna damuwata da yin ta’aziyya ga iyalai, da Mai Martaba Sarkin Bungudu, da al’ummar Bungudu biyo bayan harin ‘yan bindiga na makon jiya.
“Wannan jarabawace daga Allah Madaukakin Sarki, da ya ke jarabtar bayinsa. Gwamnatin jihar na sadaukar da kudade da kokari don kawo karshen barazanar ‘yan bindiga.
“Ina rokan kowa da kowa da a yi hakuri, domin wannan lamarin yana bukatar juriya da yawaita addu’a.
“Ina addu’ar Allah Ya bai wa iyalai hakurin jure wannan rashi. Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasu.
“Za mu ci gaba da ba wa wadanda suka jikkata dukkan taimakon da ya dace, kuma za mu yi iya bakin kokarinmu don ganin an kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su lafiya.”
A nasa martani, Mai Martaba Sarkin Bungudu ya gode wa Allah bisa bai wa Jihar Zamfara Gwamnan da ke da damuwar al’umma kuma ke yin dukkan abin da zai yiwu don kawo karshen rashin tsaro.














