ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yan Bindiga Sun Sace Dattawan Zamfara 50 Yayin Taron Sulhu A Cikin Daji

by Sulaiman and Hussein Yero
3 months ago
Zamfara

Akalla dattawa 50 daga kauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara ne aka yi garkuwa da su yayin wani zaman sulhu da suka yi da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Jammo, wanda ke iko da dajin Muntsira da ke Maradun.

Da yake zantawa da LEADERSHIP kai tsaye, shugaban karamar hukumar Maradun, Hon. Bello Dosara, ya ce dattawan kauyen sun gana da shugaban ’yan bindigar ba tare da amincewar gwamnati ba.

Ya ce, “Ni ne babban jami’in tsaro na Maradun, ya kamata su tuntuɓe ni a kalla. Babu wanda ya sanar da ni saboda sun san gwamnatin jihar Zamfara karkashin Gwamna Dauda Lawal ta haramta tattaunawa da ’yan bindiga.

ADVERTISEMENT

“Yanzu haka na karanta wani rahoto da ya ce mutum 11 ne aka saki, amma ‘yan mintuna kaɗan da suka wuce kafin kiran wayarka, an tabbatar min cewa dattawa 12 aka saki, saura 38 suna hannunsu,” in ji Dosara.

Ya kara da cewa, “Ya saki mutum 12 ɗin ne domin su je su sanar da al’umma abin da ya faru.”

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Shi ma wani shugaban matasan al’ummar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin, yana mai cewa shugaban ’yan bindigar Jammo ya kuma hana mutanen kauyen zuwa kasuwar yankin.

Ya bayyana cewa shugaban ’yan bindigar ne ya nemi a yi sulhu bayan an kashe ɗaya daga cikin yaransa a wani samamen sojoji da aka kai a kauyen Kandare kwanan nan.

Zamfara
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Zamfara
Hussein Yero
+ posts Bio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Kudirin Yaki da ‘Yan Ta’adda Ba Tare Da Sulhu Ba
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamnan Zamfara Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro Bisa Ƙwato Ɗarurruwan Shanu
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Ɗan Takarar Sanata A Zamfara Ya Koka Kan Yi Wa Rayuwarsa Barazana
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Abdulaziz Yari Ya Bukaci Limamai Su Ƙara Addu’a Kan Yaƙi Da Ƴan Bindiga A Zamfara

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Fara Wani Aikin Hanyar Ruwa A Kogi Mafi Tsawo Na 3 A Duniya

Kasar Sin Ta Fara Wani Aikin Hanyar Ruwa A Kogi Mafi Tsawo Na 3 A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.