Wani rukunin masana kimiyya na kasar Sin sun kirkiri na’urar gwaji samfurin “Jiuzhang 4.0” mai karfin lissafi da ya kafa sabon tarihi a duniya. “Jiuzhang 4.0” na amfani da fasahar haske don gudanar da lissafi cikin matukar sauri, kamar dai yadda aka wallafa hakan a jiya Laraba a mujallar kimiyya ta “Nature”.
Tawagar masu binciken karkashin jagorancin jami’ar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ko USTC, sun yi nasarar samar da na’urar gwajin, wadda ta cimma nasarar warware sarkakiyar lissafin “Gaussian boson”, da saurin da ya ninka sau 10 zuwa 54, na wanda a baya kwamfutoci mafiya sauri a duniya suka taba yi wajen warware sanannen lissafin. (Saminu Alhassan)
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
ADVERTISEMENT