Amadou Magagi, masanin harkokin cinikayya da tattalin arziki na kasar Niger, ya bayyana manufar kasar Sin ta soke haraji kan kayayyakin kasashen Afrika 53 da ke da huldar diplomasiyya da ita, a matsayin wadda ta wuce batun alfanun cinikayya, inda ya ce tana nuna dadadden kudurin Sin na samun ci gaba na baya daya, da dunkulewar tattalin arzikin duniya da hadin gwiwa bisa ka’idojin mutunta juna da daidaito da moriyar juna.
Amadou Magagi, masani a cibiyar bunkasa cinikayya da masana’natu ta Niger, ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, manufar ta bayar da damar aiwatar da alkawarin da aka yi karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, na tallafa wa ayyukan masana’antu a Afrika da karfafa shigar nahiyar cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya da kirkiro karin damarmaki ga harkokin kasuwanci na nahiyar.
Da yake bayani game da alfanun da ake sa ran Niger za ta samu, Amadou Magagi ya bayyana manufar a matsayin wata muhimmiyar dama ta musammam.
Ya ce Niger tana da dimbin amfanin gona da dabbobi da albarkatun karkashin kasa, haka kuma tana da karfi a bangarorin da suka shafi ridi da gyada da gurjiya da gam da aya da kayayyakin dabbobi da kuma kayayyaki masu daraja. Ya ce samun damar shiga katafariyar kasuwar Sin za ta taimaka wajen kara yawan abubuwan da Niger ke fitar wa da inganta sarrafa albarkatu a cikin gida da kuma kirkiro karin guraben ayyukan yi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














