ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matakan Takala Na Japan: Rashin Sanin Tarihi Ko Rashin Girmama Shi?

by Sulaiman and CGTN Hausa
9 months ago
Japan

A baya-bayan nan, Japan tana ta aiwatar da wasu matakai na takalar fada da kokarin mayar da hannun agogo baya dangane da nasarar da aka samu cikin lokaci mai tsawo, wanda nake ganin ganganci ne ko wasa da wuta.

Shin rashin sanin tarihi ne ko kuma rashin girmama tarihi da nasarar da aka samu ne ke ingiza Japan?

Duk wanda ya san yanayin tafiyar da huldar diplomasiyya, ya san cewa, kowace kasa na da inda ta ja layi. Don haka, kowa ya san cewa, batun Taiwan, wani batu ne da Sin ta sha jan kunne a kai, kuma sanin kowa ne, yankin Taiwan wani bangare na Sin da take nanata cewa, babu wanda zai iya balle shi, kuma ba makawa kasar za ta cimma burinta na dunkule dukkan yankunanta wuri guda.

ADVERTISEMENT

Radadi da wahalhalu da asarar da aka yi sakamakon yakin duniya na biyu, abu ne da ya kamata ya zama izina da darasi ga kasa da kasa, ciki har da Japan. Kana nasarar da aka samu bayan yakin, muhimmin abu ne da ya kamata a girmama kuma a daukaka. Japan ta mika wuya ba tare da sharadi ba, kuma ta amince da Sanarwar Potsdam, inda ta yi alkawarin za ta cika dukkan ka’idojin da sanarwar ta zayyana, kuma ta mayar da yankin Taiwan ga Sin ba tare da wani sharadi ba. Amma kalaman da aka ji sabuwar firaministar kasar na furtawa, da ma wasu ’yan siyasar kasar, sun saba wa haka, har ma da dokokin MDD.

Shin Japan ba ta son girmama alkawarin da ta yi ne? Ko ba ta girmama sadaukarwar da magabata suka yi?

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Har ila yau a baya-bayan nan, sojojin Japan sun yi ta kawo tsaiko ga atisayen sojojin kasar Sin da aka saba yi, a gabashin mashigar Miyako, bayan an riga an sanar da shirin atisayen tun kafin lokacin. Halin da Japan take nunawa a baya bayan nan, yunkuri ne na kawo tsaiko ga zaman lafiyar da ake mora a yankin, kuma bisa dukkan alamu, kokari take ta dawo da ra’ayin amfani da karfin soji. Sai dai, ya kamata ta gane cewa, duniya ta sauya, kuma munanan matakanta ba za su je ko ina ba, domin Sin na da karfin kare kanta.

Har kullum burin kasar Sin shi ne, wanzuwar tsaro a cikin gida da zaman lafiya da lumana da makwabtanta da shiyyarsu da ma duniya baki daya, ba don ba ta da karfin kare kanta ba, sai don ta fi ganin zaman lafiya a matsayin abun da zai amfanawa kowa, kuma shi ne muradin mafi rinjayen al’ummar duniya.

Japan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa
Japan
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Ma’aikatar Wajen Sin: Shin Japan Tana Yunkurin Ci Zarafin Sin Tare Da Haifar Da Tashin Hankali

Ma’aikatar Wajen Sin: Shin Japan Tana Yunkurin Ci Zarafin Sin Tare Da Haifar Da Tashin Hankali

LABARAI MASU NASABA

Japan

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Japan

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.