ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da sabon tsarin doka da ƙa’idoji domin inganta harkar gine-gine a Nijeriya, da nufin kawo ƙarshen yawaitar rugujewar gine-gine, da daƙile ayyukan maginan bogi da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin gine-gine a faɗin ƙasar. Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ya ce sabon tsarin zai samar da ingantaccen tsarin sa ido kan harkar gine-gine tare da ƙara kare rayuka da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin da ya karɓi shugabannin Majalisar Kula da Aikin Injiniya ta Nijeriya (COREN) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Sadiq Zubair Abubakar. Ya ce ma’aikatar za ta gabatar da daftarin tsarin ga masu ruwa da tsaki kafin ƙarshen watan Yuli domin tattaunawa, kafin daga bisani a miƙa shi ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) domin amincewa.

A cewar Darma, sabon tsarin zai daidaita ayyuka da nauyin ƙungiyoyin ƙwararru a fannin gine-gine tare da tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin gine-gine da ƙa’idodin aikin ƙwararru. Ya nuna damuwa cewa raunin tsarin sa ido ya bai wa mutanen da ba su cancanta ba damar gudanar da ayyukan gine-gine, lamarin da ya haddasa gine-gine marasa inganci da yawaitar rugujewarsu a sassan ƙasar. Ya jaddada cewa gwamnati ta kuduri aniyar tsaftace fannin da dawo da ƙwarewa da bin ƙa’ida.

ADVERTISEMENT

A nasa jawabin, Shugaban COREN, Farfesa Sadiq Zubair Abubakar, ya taya ministan murnar naɗin da aka yi masa, yana mai bayyana ƙwarin gwiwa cewa zai inganta harkar gidaje da gine-gine ta hanyar ƙarfafa tsarin sa ido da bin doka. Ya kuma gayyace shi zuwa Taron Injiniyoyi karo na 34, wanda ake sa ran zai haɗa ƙwararrun injiniyoyi da masu fasaha tsakanin 8,000 zuwa 9,000 daga Nijeriya da ƙasashen waje, inda za a tattauna batutuwan tsaron jama’a, bin ƙa’idoji da kuma sabbin hanyoyin hukunta masu karya dokokin gine-gine.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64
  • Abubakar Sulaiman
    Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

MASU ALAKA

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark
Manyan Labarai

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

July 13, 2026
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Matatar Sarrafa Ma’adanin Lithium Ta $200m A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Matatar Sarrafa Ma’adanin Lithium Ta $200m A Zamfara

July 13, 2026
Next Post
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026
Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

July 13, 2026
Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026
Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

July 13, 2026
Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

July 13, 2026
Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 13, 2026
Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.