Kwanan nan, an kammala gasar nuna kwarewar sana’o’i ta duniya karo na 48 cikin nasara a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. A fagen gasar, tawagar Sin ta shiga sahun gaba a duniya a fannoni da dama, tun daga injin da na’ura mai kwakwalwa ke sarrafawa zuwa mutum-mutumin inji na masana’antu, da fasahar walda, gami da aikin gini bisa fasahar zamani. Amma abin da ya fi jawo hankula shi ne, tsarin da Sin take da shi waje raya wadannan fasahohi, da rawar da wannan tsarin ke takawa ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, matakin da zai canza makomar matasan Afirka.
Kwarewar da Sin ta nuna a gasar ta dogara ce kan cikakken tsarin horar da kwararrun fasaha. Ya zuwa yanzu, makarantun sana’o’i na Sin sun wuce 10,000, kana daliban da ke karatu a cikinsu yawansu ya wuce miliyan 33, ban da haka, jimillar kwararrun fasaha a duk kasar ta haura miliyan 200. Daga cikinsu kwararrun fasaha mafi hazaka sun wuce miliyan 72. Ruhin wannan tsari shi ne, kwarewar fasaha ba tana ginuwa a kan “hanyar da za a bi idan babu sauran mafita” ba ce, sai dai a kan turbar samun “mafita mafi kyau”. A Sin, adadin samun aikin yi na daliban da suka kammala makarantun fasahar ya dade yana zarce sama da kashi 95% a ko wace shekara. Sin ta tabbatar da cewa, matukar ana mallakar fasaha, to za a rika samun mafita.
Matasan Afirka ma sun hau wannan hanya.
A wannan gasar, Afirka ta Kudu ta tura masu fafata gasar su 29 don shiga rukunan fasaha 27 na gasar. Kasar Namibia ta tura matasa 17 don fafatawa a ayyuka 16. Kana Uganda ma ta tura masu fafatawa 3 a fagen jinya da walda da dafa abinci. Duk da cewa yawan masu shiga gasar ba shi da yawa, amma kasashen Afirka sun fara bayyana karfinsu a wannan bangare. Sin na son raba damammaki da more fasahohinta da kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, don tabbatar da huldar hadin gwiwa mai amfani ga kowa. Hadin gwiwar fasaha na zama sabuwar hanyar hadin gwiwar Sin da Afirka.
Afirka na da dimbin matasa. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, sama da kashi 60% na al’ummar yankin kudu da hamadar Sahara na Afirka suna kasa da shekaru 25 da haihuwa ne. Zuwa shekarar 2030, rabin yawan karin ’yan kwadago na duniya da za a samu zai fito ne daga wannan yankin. Amma, kashi 98% na ’yan Afirka da ba su kai shekaru 18 ba, ba su mallaki fasahar STEM, wato kimiyya da fasaha da injiniyanci da lissafi bayan kammala karatunsu ba. Abin da Afirka ke matukar bukata shi ne kwarewar “Fasahohin sana’o’i”. Hakan ya sa hadin gwiwar Sin da Afirka samun wata sabuwar hanya mafi dacewa.
Cibiyar Luban wani mataki ne dake karkashin wannan tsari na hadin gwiwa. Tun daga shekarar 2016, Sin ta kafa cibiyoyin Luban a kasashe da dama a Afirka, inda kasar ta ba da horon sana’o’i kamar kera kayayyaki ta amfani da injin da na’ura mai kwakwalwa ke sarrafawa da aikin lantarki da na walda da sarrafa mutum-mutumin inji da sauransu. A Djibouti, cibiyar Luban ta bude sashen kula da harkokin jirgin kasa, don horar da kwararrun fasaha na cikin kasar domin layin jirgin kasa mai hada Addis Ababa da Djibouti. A Masar, cibiyar Luban ta bude kwasa-kwasan sarrafa inji mai kwakwalwa da mutum-mutumin inji na masana’antu. A Kenya kuwa, cibiyar Luban tana ba da horo a kan fasahohin zamani ta yadda matasan za su zama masu fasaha bayan kammala samun horo.
’Yan kasar Sin da suka fafata gasar, wadanda suka tsaya kan dandalin lambar yabo a wannan gasa, da kuma matasan Afirka da suke samun horo a cibiyar Luban, dukkansu sun ci gajiyar tsarin horar da kwararrun fasahohin sana’o’i da Sin ta aiwatar. Sin ta dauki shekaru da dama wajen tabbatar da bai wa matasa makoma mai kyau bisa wannan mataki, kuma a yanzu tana raba dabarunta ga kasashen Afirka ta hanyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Samun lambobin zinari a gasar ya sheda nasarar wannan tsari, amma ma’ana mafi zurfi ita ce a ba mutane da yawa damar mallakar fasahohin.
Fasaha ba ta da iyaka, kuma ba za a bar kowa a baya ba a wannan bangare. Lokacin da masu sana’a na Sin ke samun lambobin a dandalin duniya, matasan Afirka ma za su iya koyon sana’a iri daya, ta hakan za su sami mafitarsu.(Marubuciya: MINA)














