Kotun sojoji da ke Abuja ta sake ɗage ranar yanke hukunci kan amincewa da bayanan da wasu jami’an sojoji da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki suka bayar a matsayin shaida.
An tsara yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, amma yanzu an ɗage hukuncin zuwa Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2026.
Ana gudanar da shari’ar ne a Scorpion Officers’ Mess da ke Asokoro, Abuja, ƙarƙashin jagorancin Air Vice Marshal H.I. Alhaji.
Wannan shi ne karo na huɗu da aka ɗage yanke hukuncin.
Kotun ba ta bayyana dalilin sake ɗage ranar yanke hukuncin ba.
Lauyoyin da ke kare waɗanda ake zargi, sun ƙalubalanci bayanan, suna zargin cewa an tilasta wa ko matsa wa wasu daga cikin jami’ansu bayar ko su sanya hannu kan bayanan.
Sai dai masu gabatar da ƙara sun gabatar da hujjojin da suke cewa jami’an sun bayar da bayanan ne da yardarsu.
Hukuncin kotun zai fayyace ko za a amince da waɗannan bayanai a matsayin shaida a shari’ar da ake yi.














