Wani matashi mai shekaru 18, Abdullahi Aminu, ya rasu bayan ya faɗa cikin wani kududdufi a Kofar Gabas, a ƙaramar hukumar Danbatta ta Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, 11 ga watan Agusta 2026, da misalin ƙarfe 3:28 na rana, bayan mahaifin matashin, Aminu Lawan, ya kira hukumar domin neman agaji.
Jami’an kashe gobarar Danbatta sun isa wurin kuma suka ciro Abdullahi daga cikin ruwan a sume, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Daga nan aka miƙa gawarsa ga Sakataren Hakimin Danbatta, Alhaji Baba Ado Sarkin Bai, domin ɗaukar matakin da ya dace.
Hukumar ta jajanta wa iyalan mamacin tare da gargaɗin jama’a da su yi taka-tsantsan a kusa da kududdufai, koguna da sauran wuraren da ruwa ke kwanciya, musamman a lokacin damina.












