Tsohon firaministan kasar Sin, Zhu Rongji, ya rasu sakamakon rashin lafiya yana da shekaru 98 a duniya, a birnin Beijing da misalin karfe 11:06 na safiyar yau Laraba.Zhu ya taba zama mamba a zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitocin koli na 14 da 15 na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS).
Wata sanarwa game da rasuwarsa da aka fitar cikin hadin gwiwa a tsakanin kwamitin kolin JKS, da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalisar gudanarwa ta kasa, da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar Sin, ta yaba wa Zhu a matsayin nagartaccen dan jam’iyyar, kuma gogaggen dan gwagwarmayar gurguzu mai biyayya, kana fitaccen dan juyin-juya-halin ’yan kwadago kuma dan siyasa, sannan jagoran jam’iyya da kasa baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














