Mazauna birnin Minna da kewayensa a Jihar Neja sun bayyana fargaba da takaicinsu kan yawaitar hare-haren da masu haƙar ma’adanai ke kaiwa, biyo bayan wani sabon rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata wasu a ƙarshen makon nan. Lamarin ya haifar da gagarumin zaman ɗar-ɗar a tsakanin al’ummomin da ke maƙwabtaka da wuraren haƙar ma’adanan a cikin birnin da kewayensa.
Bayanai sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne a yayin da aka samu sa-in-sa tsakanin matasan yankin da gungun masu haƙar ma’adanan kan batun mamaye filaye da ɓarnatar da muhalli, lamarin da ya rikiɗe zuwa faɗan da aka yi amfani da miyagun makamai.
Mazauna yankin sun bayyana cewa masu haƙar ma’adanan waɗanda da yawansu baki ne da ke gudanar da ayyukansu ba bisa ƙa’ida ba sun daɗe suna cin karensu babu babbaka tare da tsoratar da mutanen gari.
Shugabannin al’umma a Minna sun koka da cewa ayyukan waɗannan masu hakar ma’adanai sun zama babbar barazana ga tsaro da rayuwar iyalansu, inda suka buƙaci Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da hukumomin tsaro da su gaggauta rufe duk wasu haramtattun wuraren haƙar ma’adanai a kewayen birnin.
Sun yi gargaɗin cewa idan hukumomi ba su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan lokaci ba, matsalar ka iya ta’azzara ta haifar da mummunan faɗan ƙabilanci ko na ɗaukar fansa.
Rundunar Ƴansandan Jihar Neja ta tura dakarun tsaro domin kwantar da tarzomar tare da tabbatar da tsaro a yankunan da, abin ya shafa, yayin da take ci gaba da gudanar da bincike domin cafke waɗanda ke da hannu a kisan mutanen biyu.
Rundunar ta buƙaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu, tana mai alƙawarin cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi kamar yadda doka ta tanada.














