A ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, manyan ƙasashe a fagen ƙwallon ƙafa na nahiyar Afrika, wato Nijeriya (Super Falcons) da takwararta Afirka Ta Kudu (Banyana Banyana), za su fafata a wasan share fagen neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya na Mata na shekarar 2027, wanda za a gudanar a ƙasar Brazil.
Wannan wasa da zai gudana a ranar Alhamis na da matuƙar muhimmanci, musamman ga Nijeriya, domin nasara a kan Afirka Ta Kudu zai ba ta damar ci gaba da riƙe kambunta na zama ƙasar Afirka tilo da ba ta taɓa kasa samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya na Mata ba tun lokacin da aka fara gudanar da gasar a shekarar 1991. Dukkan ƙasashen biyu suna fatan samun wannan gurbi bayan an fitar da su daga gasar kofin nahiyar Afirka a mabanbantan wasanni.
Wannan wasan zai sake farfaɗo da hamayya mai tsanani a tsakanin ƙasashen biyu, duba da yadda a baya Nijeriya ta hana Afirka Ta Kudu samun gurbin shiga gasar Olympics ta Paris ta shekarar 2024, bayan da ta doke ta a zagaye na ƙarshe na neman tikitin shiga gasar.
Bugu da ƙari, Nijeriya ta sake yin galaba a kan Banyana Banyana ta Afrika Ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe a gasar WAFCON da aka gudanar a shekarar 2024, lamarin da ya ci gaba da jaddada adawa tsakanin waɗannan manyan ƙasashe a fagen ƙwallon ƙafan mata na nahiyar Afrika.














