ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Wajen Sin Ya Gana Da Manema Labarai Kan Manufofi Da Alakar Kasar Da Ketare

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gudanar da taron manema labaru yau Lahadi, a gefen taro na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14, inda ya amsa tambayoyin ‘yan jarida na gida da waje kan manufofin kasar Sin na harkokin waje da huldar kasar da kasashen ketare.

A yayin taron, Wang Yi ya bayyana cewa, “abokantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta yi tsayin daka wajen jure wa jarabtar da ake samu daga sauye-sauyen yanayin kasa da kasa, wanda hakan ya nuna kuzari mai karfi.” Daga ranar 1 ga watan Mayu, kasar Sin za ta fara aiwatar da matakin soke harajin kwastam baki daya a kan kayayyakin da ake biyan haraji a kansu wadanda ake shigo da su daga Afirka.

Kazalika, bisa babban mataki na bude kofar kasar Sin, bangaren Sin zai yi amfani da “cire” harajin wajen bunkasa “karin” cinikayya, da cimma nasarar “rubanya” kyautata rayuwar jama’a, da kuma barin babbar kasuwar kasar Sin ta samar da damammaki ga Afirka.

ADVERTISEMENT

Ban da haka,Wang Yi ya bayyana cewa, a duniyar yau, dimbin kalubalen da suka shafi duniya baki daya na kara bullowa daya-bayan-daya, kuma tsarin bangarori daban-daban na fuskantar kalubale masu tsanani. Shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta zo a kan lokaci, kuma cikin hanzari ta samu goyon baya da amsa daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 150. Kasar Sin tana kira ga karin kasashe da su shiga a dama da su tare da goyon bayan shawarar ta inganta jagorancin duniya, da yin aiki kafada-da-kafada don farfadowa da kiyayewa, da kuma karfafa MDD.

Duk a wajen taron, Wang Yi ya yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a yankin Gabas ta Tsakiya domin kare ta’azzarar rikicin da kaucewa yaduwarsa. Ya ce amfani da karfi ba ita ce hanyar warware matsaloli ba, yana mai cewa hakan sabon kiyayya zai haifar. Ya kuma bayyana cewa, kasashe masu tasowa sun zama muhimmin karfin dake ingiza rarrabuwar iko a duniya. Game da dangantakar Sin da Amurka kuma, ya ce ya kamata kasashen biyu su mutunta juna, su kuma rungumi hulda tare cikin lumana.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Wang Yi ya kara da cewa, shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama na da nufin shaida wa duniya cewa makiya bil’adama ba a junansu suke ba, amma su ne yaki, fatara, yunwa, da rashin adalci. Don shawo kan wadannan kalubalen, ba za mu iya dogaro da kokarin daidaikun mutane kadai ba, a’a, wajibi ne mu zama tsintsiya madaurinki daya da kuma yin hadin gwiwa. A zamanin yau, mutane daga dukkan kasashe suna kara fahimtar alfanun zamani da karfin gaskiya da ke tattare da manufar al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama.

Wang ya kuma ce, katafariyar bunkasar da kasar Sin ke yi ba za ta taba bin tsohuwar hanya ta nuna karfin iko na babakere da fadada kasa ba, sai dai ma ta bi hanyar samun ci gaba cikin lumana, da sa kaimi ga dukkan kasashen duniya wajen gina duniya mai cike da zaman lafiya mai dorewa, da wadata, da tsafta, da kuma kyau. (Abdulrazaq Yahuza)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Darussa Daga Ramadan Na (1)

Darussa Daga Ramadan Na 15: Kusancin Allah Da Amsar Addu’a A Ramalana

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.