Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a Igbokoda, Jihar Ondo.
Mutanen da suka rasun sun haɗa da ma’aikatan jirgin guda biyar da fasinjoji 20.
Jirgin yana kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas ne lokacin da ya yi hatsari.
NAF ta tabbatar da cewa babu wanda ya tsira.
Ma’aikatan jirgin guda biyar:
1. Squadron Leader MI Aburime – Kyaftin ɗin jirgin
2. Squadron Leader AP Man-Ugwueje – Mataimakin kyaftin
3. Flight Lieutenant IS Bako – Mataimakin kyaftin
4. Warrant Officer Abubakar A – Ma’aikacin gyaran jirgi
5. Corporal Uguru HC – Ma’aikacin gyaran jirgi
Fasinjoji 20:
6. Flight Lieutenant TL Lazarus7. Flight Lieutenant M Akinloye
8. Flying Officer IM Adeshina
9. Master Warrant Officer Onwuka F
10. Master Warrant Officer Matini BA
11. Warrant Officer Nuhu FS
12. Flight Sergeant James RB
13. Flight Sergeant Mohammed AI
14. Sergeant Ani AE1
5. Sergeant Izibenikien SI
16. Sergeant Alafuka C
17. Sergeant Mbadugha AN
18. Lance Corporal Ugwuba FC
19. Lance Corporal Eledan GE
20. Mrs Ezeh Nneka
21. Godstmine Tarabina
22. Joy Micheal
23. Sunday Micheal
24. Ukeme David
25. Gideon Omotola
Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.
NAF ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, inda ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a sabbin bayanai yayin da bincike ke gudana.














