Matatar man fetur ta Dangote na shirin ninka yawan ma’aikatanta, yayin da ta ke shirin ƙara yawan ƙarfin tace mai daga ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekarar 2029.
Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote mai kula da harkokin mai, iskar gas da takin zamani, Edwin Devakumar ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da aka kai matatar da ke Legas.
Ya ce mafi yawan sassan matatar za su buƙaci ƙarin ma’aikata, sai dai sashen sarrafa ruwa yana da isasshen ƙarfin gudanar da aiki a halin yanzu.
Kamfanin na neman tara kusan Naira tiriliyan 2.2, kwatankwacin dala biliyan 1.6, daga masu zuba jari domin aikin faɗaɗa matatar.
Mafi ƙarancin hannun jarin da za a iya siya na matayar shi ne kaso 10, wanda darajarsa ta kai Naira 5,250, kuma masu zuba jari sun karɓi tayin hannu biyu.
Devakumar, ya ce kuɗin faɗaɗa matatar ba zai kai na farkon ginin matatar ba, saboda akwai wasu muhimman abubuwa da aka riga aka samar.
Haka kuma, sabon ɓangaren zai yi kama da tsarin matatar da ake da ita.
Kamfanin Dangote ya kuma shirya ƙara yawan takin zamani da yake samarwa a shekara daga tan miliyan uku zuwa tan miliyan 12.
A cewar bayanan kamfanin, ya samu ribar dala biliyan 1.8 bayan cire haraji daga kuɗaɗen shiga da suka kai dala biliyan 13 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.














