Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar wasu da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka rasu a hannun jami’an Hukumar Tsaron NSCDC a Minna, Jihar Neja.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce rayuwar kowane ɗan Nijeriya tana da muhimmanci, kuma bai kamata wani ya mutu a hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi ko rashin kulawa ba.
Shugaban ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su binciki yadda aka kama mutanen, yanayin da suke ciki lokacin da aka tsare su, yadda aka kula da su, yawan mutanen da aka tsare da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su kafin mutuwarsu.
Tinubu ya ce duk jami’in da aka gano cewa ya taimaka wajen mutuwar mutanen ta hanyar cin zarafi ko sakaci, ya kamata a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ya kuma umarci Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da shugabannin NSCDC da su ba masu bincike cikakken haɗin kai, tare da tabbatar da cewa babu jami’in da zai kawo cikas wajen binciken.
Shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Ya ce gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.
Tinubu ya jaddada cewa yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba dole ne a gudanar da shi bisa doka tare da mutunta haƙƙi da mutuncin mutanen da ke tsare a hannun gwamnati.














