ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
42 minutes ago
Borno

Yadda hukumomin tsaro a Nijeriya suka yi kawancen ceto dalibai da malaman makaranta a jihar Oyo daga hannun gawurtaccin ‘yan ta’adda ba tare da biyan kudin fansa ba ya nuna irin nasarar da jami’an tsaro ke kara samu a yaki da ta’addanci.

A kwanan nan hedikwatar tsaro ta bayyana cewar, dakarun soji sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 665 tare da kama sama da mutane 1,000 da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci daban-daban, an kuma kubutar da mutane sama da 900 da aka yi garkuwa da su tare da tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu aikata manyan laifuka

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewar farmakin ya nuna a fili idan aka ci- gaba da matsawa kungiyoyin ‘yan ta’addar lamba ta hanyar kai hare- hare kai tsaye kan maboyarsu, tarwatsa hanyoyin samun kayan aiki da kamo masu taimaka masu, zai raunana karfin su tare da samun galabar kawar da su.

ADVERTISEMENT

LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa a ranar 15 ga Mayu 2026, ‘yan ta’adda sun kai hari makarantu uku da suka hada da makarantar rainon yara da furamare ta Baptist da ke Yawota da sakandiren al’umma ta Community High School da kuma makarantar furamare ta L.A, dukkansu a Ahoro-Esinele da ke Karamar Hukumar Oriire a jihar Oyo a inda suka yi garkuwa da mutane 46 wadanda suka kunshi dalibai 39 da malamai bakwai.

Sai dai abin takaici ‘yan ta’addan sun kashe daya daga daga cikin malaman, Adegboye Adesiyan a nan take a lokacin harin a yayin da wani malamin Michael Oyedokun, ya rasa ransa a yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutanen. Hakan ya sa adadin wadanda aka sako daga baya ya ragu zuwa mutane 44.

LABARAI MASU NASABA

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su, wadanda suka shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan ta’addan sun shaki iskar ‘yanci ne a ranar Juma’a da ta gabata bayan wani samame na tsawon kusan wata guda da hukumomi suka ce an gudanar bisa ingantattun bayanan sirri.

Aikin ya hada jami’an tsaro daga ofishin mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, hukumar tsaro ta farin kaya, rundunar sojin Nijeriya da kuma ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro.

Shugaba Bola Tinubu, ya yi maraba da sakin wadanda aka ceto, ya kuma yaba da abin da ya kira kwazo da jarumtar da jami’an tsaron suka nuna wajen gudanar da aikin, haka kuma ya bayyana cewa an kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan a yayin da aka kama mutane takwas daga cikinsu.

Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an yi wa wadanda abin ya shafa adalci, haka kuma ya umarci hukumomin ba da agajin gaggawa da su hada kai da Gwamnatin jihar Oyo domin samar da dukkan kulawar lafiya da sauran tallafin da ake bukata ga daliban da malamansu da aka ceto.

A nasa bangaren, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya jinjinawa kwazon jami’an tsaro kan nasarar da suka samu ta hanyar nuna kwarewa wajen ceto dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su tare da godewa Shugaba Tinubu kan irin goyon bayan da ya bayar wajen samun gagarumar nasarar.

A kan biyan kudin fansa kuwa, Gwamnan ya jaddada cewa ba a biya ko sisi a matsayin kudin fansa ba kafin a sako wadanda aka yi garkuwa da su tare da jaddada cewar kokari ne na hukumomin tsaro wadanda suka cancanci a yaba masu.

Haka kuma a sanarwar da kakakin Runduna ta 2 ta Sojin Nijeriya da ke Ibadan, Jonah Danjuma, ya fitar, ya ce ceto mutanen da aka yi garkuwa da su ya biyo bayan tsararrun hare- haren sama da wata guda da suka kai kan shugabannin kungiyar ‘yan ta’addan, hanyoyin samar musu da kayan aiki da kuma masu ba su bayanan sirri.

Ya ce aikin hadin guiwar jami’an tsaron ya mayar da hankali ne kan gano jagororin da suka shirya sace daliban da malamansu, tare da tarwatsa cibiyoyin aikinsu da maboyarsu da ke cikin daji.

Ya ce “Kamun da aka yi ya tarwatsa tsarin ‘yan ta’addan bakidaya, ya jefa su cikin matsin lamba mai tsanani wanda a karshe ya tilasta wa ‘yan ta’addar sakin daliban da malamansu ba tare da gindaya ko wane irin sharadi ba a bisa ga wutar da suka sha.”

Kakakin rundunar ya kara da cewa an tsara aikin cikin matukar tsanaki domin tabbatar da an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya tare da kaucewa jawo asarar rayuka ko barna ga fararen hula, sai dai ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi asarar rayuka a yayin gudanar da harin, amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu ko kuma ko su waye ba.

Sai dai bayan kasa da awanni 24 da jami’an tsaro suka kubutar da dalibai da malaman, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace shugaban makarantar firamare ta Nomadic Basic School da ke Igbojaye, a karamar hukumar Itesiwaju da ke jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar an yi garkuwa da Matthew Owoade dan shekaru 60 ne a ranar Juma’a a kan hanyarsa ta dawowa daga gona, lamarin da ya sake tayar da hankalin mazauna yankin a daidai lokacin da suke murnar sako dalibai da malaman su.

Sakataren kungiyar malamai ta NUT na jihar Oyo, Salami Olukayode wanda ya tabbatarwa manema labarai da faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce an dauki matakan da suka dace domin tabbatar da sakin wanda aka yi garkuwa da shi.

Haka ma a Jihar Zamfara, jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar barayin daji a mabambantan hare- hare da suka kai a jihar wadda ta yi kaurin suna da bahaguwar matsalar tsaro lamarin da ya kara sanyaya zukatan al’ummar jihar.

Kisan gillar rikakken dan ta’adda kuma shugaban barayin daji, Kachalla Sani Yellow wanda ke da karfin iko tare da addabar al’ummar ciki da wajen jihar Zamfara da aka yi kwanan nan babbar nasara ce a yaki da ta’addanci a Nijeriya.

Kwararren masanin harkokin tsaro Zagazola Makama ya bayyana cewar an kai harin da ya kawo karshen ta’addancin Yellow ne da rana tsaka a lokacin da rahotanni suka nuna cewa shugaban barayin na gudanar da wasu harkoki a cikin kasuwar da ke cike da jama’a.

Bayanai sun nuna cewar mahara sun yi masa kwanton bauna ne kafin su bube masa wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take wanda labarin ya yadu kamar wutar daji a bisa ga yadda jama’a suka cika da murnar halaka hatsabibin barawon dajin.

Sai dai an samu sabanin bayanai kan yadda aka kashe shugaban ‘yan ta’addan wanda majiyoyin cikin gida da jami’an tsaro suka bayar da mabanbantan bayanai game da yadda fitaccen dan bindigar ya hadu da ajalinsa.

Rahotanni sun ce an harbe shi har lahira ne a ranar Juma’a da nisalin karfe 10:00 na safe a kasuwar Dan- Jibga da ke karamar hukumar Anka a yayin da wata kungiyar mahara da suke adawa da juna dauke da makamai wadanda ake zargin mabiyan fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Dogo Gide ne suka kai masa hari.

Mazauna yankin da suke sane da yadda kungiyoyin ‘yan bindiga ke gudanar da ayyukansu sun bayyana lamarin a matsayin wata alama ta kara tsanantar rikicin cikin gida tsakanin kungiyoyin ‘yan bindigar wadanda ke fafatawa domin kwace iko, fadada tasiri da mamaye yankuna daban-daban a fadin jihar Zamfara.

Sai dai wasu majiyoyi kuma sun shaidawa manema labarai cewa jami’an tsaro ne da hadin guiwar jami’an sa-kai ne da aka dauko daga jihar Borno ne suka samu nasarar dakle wani hari da ‘yan bindigar suka kai wanda a yayin musayar wutar ne suka hallaka Kachalla Yellow wanda ya adabbi yankin da kisan gilla, gakuwa da mutane da satar shanu.

Koma dai yaya ne mutuwar Kachalla Yellow ta kawo karshen fargabar aika- aikarsa a bisa ga yadda ya jima yana addabar al’ummomi a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru a jihar Zamfara kuma a na danganta shi da hare-hare da dama da aka kai a wasu sassan yankin Arewa- maso- Yamma.

A yayiin da yake tsokaci kan lamarin, tsohon Dan Majalisar Dattawa a Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya kamata a kawar da fitattun shugabannin ‘yan bindiga, Bello Turji da Ado Aleru kamar yadda aka kashe shugaban barayin daji Kachalla Yellow.

Shehu Sani ya ce kashe Kachalla Sani Yellow wata babbar nasara ce a yakin da ake yi da ta’addanci a Arewacin Nijeriya kamar yadda ya wallafa a shafinsa na D da cewar “labarin kashe fitaccen kuma hatsabibin shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Yellow da jami’an tsaron Nijeriya suka yi, babbar nasara ce a yaain da ake yi da ta’addanci a yankin Arewa- maso- Yamma.

Sai dai yayin hada wannan rahoton a ranar Laraba wani bidiyo ya bulla a kafafen sada zumunta inda wani da ya kira kansa da sunan Sani Yellow ya musanta batun kisan da aka yi masa. A faifan bidiyon mai dauke da minti 1:29 da ya dauka gefen babban titi, ya aika sako kai tsaye ga Gwamnan jihar Zamfara yana cewar yana raye bai mutu ba kuma sai ta Allah ta yi.

To amma jama’a da dama a kafafen sada zumunta daga jihohin Zamfara da Katsina da suka san ‘yan ta’addan sun bayyana cewar Sani Yellow biyu ne na Zamfara wanda Kachalla ne da kuma na Katsina wanda a cewar su tabbas jami’an tsaro sun kashe shi a Zamfara. A ta bakin su tun farko an samu rudani wajen yada hoton na Katisna a matsayin na Zamfara don haka wanda ya yi bidiyo a yanzu a Katsina yake ta’addanci ba a Zamfara ba.

Bugu da kari kwanaki kadan gabanin kisan Kachalla Yellow al’ummar karamar hukumar Gummi da ke makwabtaka da Anka a jihar Zamfara sun kasance cikin farin cikin samun nasarar da jami’an sojojin Nijeriya suka yi a wani artabu da suka yi da barayin daji.

Al’ummar Gummi sun fito ne ba adadi a ranar Alhamis din makon jiya suka tarbi sojoji tare da jinjinawa dakarun Operation Fansan Yamma kan jarumtar da suka nuna bayan dawowarsu sansani daga samamen da suka yi cikin nasara, inda suka kashe ‘yan bindiga da dama a Dutsen Gidan- Hill, mai nisan kimanin kilomita 17 daga garin Gummi.

Dakarun sun nuna kwarewa da bajinta a fagen daga inda suka hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da kwato babura masu yawa da ‘yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare-hare kan al’ummomin yankin tare da  kwaso baburan zuwa hedikwatarsu ta amfani da motar sulke ta soji.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakin Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Bugu da kari a makon jiya ne rundunar soji suka samu nasarar dakile wani kadamin harin barayin daji kusan 300 a karamar hukumar Kauran- Namoda da ke Zamfara tare da kashe da dama daga cikin su kamar yadda rahotanni suka ruwaito.

A hari dakarun operation Fansan Yamma sun samu galabar halaka kwamandan ‘yan bindiga da aka fi sani da Alhaji Tukur wanda bayanai suka nuna kane ne ga gawurtaccen dan ta’adda Alhaji Shehu Bagiwaye wanda ake nema ruwa a jallo.

A kan galabar jami’an tsaro kan ‘yan ta’adda LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar a farkon wannan watan ne Hedikwatar Tsaro a Nijeriya ta bayyana cewar dakarun rundunar sojin kasa sun samu gagarumar nasara a ayyukan tsaro da suka gudanar a fadin kasar cikin watan Yuni da kuma bakidaya tsawon zango na biyu na shekarar 2026.

A cewar hedikwatar, an kashe ‘yan ta’adda 665, an kuma kama sama da mutane 1,000 da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci daban-daban, an kuma kubutar da mutane sama da 900 da aka yi garkuwa da su tare da tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu aikata manyan laifuka.

Kakakin Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a inda ya ce dakarun tsaron Nijeriya sun ci- gaba da gudanar da hadaddun hare-hare ta kasa, sama da kuma amfani da ingantattun bayanan sirri kan kungiyoyin Boko Haram, ISWAP, IPOB/ESN, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu satar danyen mai da kuma masu safarar makamai. Ya jaddada cewa rundunar sojin na ci- gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya, tabbatar da tsaro da kuma karfafa amincewar jama’a a fadin kasar.

A yankin Arewa- maso Gabas kuwa, dakarun Rundunar Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 484, sun kama mutane 370 da ake zargi, sun kubutar da mutane 595 da aka yi garkuwa da su, sannan sun karbi mayaka 38 da suka mika wuya tare da iyalansu a cikin zango na biyu na shekarar.

Ya ce daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu shi ne kubutar da fararen hula 360, galibinsu mata da yara, daga tsaunukan Mandara da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno a ranar 6 ga Yuni wadanda suka kasance a hannun ‘yan ta’adda tun bayan da aka sace su daga garin Ngoshe a watan Maris.

A yankin Arewa- maso- Yamma kuma, dakarun Rundunar Fansan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda 77, sun kama mutane 210 da ake zargi da ta’addanci tare da kubutar da mutane 153 da aka yi garkuwa da su.

Borno
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Shekara 200 Bayan Shehu Ɗan Fodiyo: Hubbarensa Na Ci Gaba Zama Wajen Ziyara Da Neman Tabarruki
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

MASU ALAKA

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.