A yayin da aka shiga damu nar bana a shekarar 2026, gwamnati a mabambantan matakai da manoma sun yi nisa a shirye- shiryen tunkarar damunar musamman domin samun yabanyar amfanin gona mai albarka.
A bisa ga yadda daminar bana ta kankama, gwamnati da manoma a yankunan Arewa- maso- Yamma, musamman a jihohin Sakkwato, Zamfara da Katsina sun yi nisa a ɗaukar matakan musamman domin tabbatar da samun wadataccen abinci duk da ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin.
Sai dai hauhawar farashin takin zamani da tsadar magunguna kashe ƙwari da jinkirin samun tallafin takin zamani daga gwamnati na daga cikin matsalolin da manoma ke fuskanta tare da ƙorafi a kai
A tsayin shekarun nan, matsalar ta’addanci da hare-haren ƴan bindiga ta yi tasiri sosai ga harkokin noma domin dubban manoma sun rasa gonakinsu, wasu kuma sun ƙauracewa noma baki ɗaya saboda fargabar hare-hare wanda hakan ya janyo raguwar amfanin gona tare da hauhawar farashin abinci a kasuwanni.
Sai dai a bana, akwai fargabar idan har gwamnati da hukumomin tsaro ba su ƙara tashi tsaye wajen yaƙi da matsalolin tsaro ba, manoma za su ci gaba da fuskantar ƙalubalen zuwa gona ballantana su noma wadataccen abinci.
A kan hakan manoma sun bayyana cewar wajibi ne gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su ƙara zage damtse wajen samar da tsaro a yankunan karkara ta hanyar tura jami’an tsaro a yankuna tare da kafa rundunonin sa-kai da ke taimakawa jami’an tsaro wajen sa ido da bayar da bayanan sirri.
A wasu yankunan an ɓullo da tsarin haɗin guiwa tsakanin manoma da hukumomin tsaro a inda ake tsara lokutan zuwa gona cikin tsari da kariya. A wasu ƙauyuka, manoma na fita gona ne a cikin rukuni-rukuni domin rage haɗarin kai hare-hare.
A yayin da aka shiga damanar manoma da dama a yankunan da matsalolin tsaro suka yi ƙamari a waɗannan jihohin na cike da fargaba abin da ke iya zuwa ya dawo a gonakin su musamman yadda ɓarayin daji ke kawo masu cikas ga zuwa gonaki da ƙaƙaba masu biyan harajin noma.
A ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tunkarar damanar bana domin samun yabanya mai albarka Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana cewa Nijeriya na kan hanya wajen tabbatar da shirin samar da takin zamani tom miliyan 1.1 a 2026 wanda ya yi daidai da buhuna kusan miliyan 22 a faɗin ƙasa wanda ɗaya ne daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙara yawan amfanin gona da kuma tabbatar da wadatar abinci a ƙasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a makon jiya a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya yaba da rawar da Ma’aikatar Kuɗii ta Ƙasa da kuma Asusun Raya Noma na Ƙasa ke takawa.
A kan hakan ya yaba da ƙoƙarinsu wajen ƙarfafa tsarin samar da taki a faɗin ƙasa tare da faɗaɗa damar da ke ga manoma wajen samun kayan aikin noma, tare da ciyar da manufofin gwamnatin a gaba ta fuskar tabbatar da wadatar abinci.
Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa tsare-tsaren kwangila na musamman da aka yi kan muhimman kayan haɗa taki sun haifar da ajiyar kuɗi har naira biliyan 61.58 a shekarar 2026 kaɗai, lamarin da ya taimaka wajen rage tsadar taki da kuma sauƙaƙa shigarsa a hannun manoma a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa yanzu Nijeriya na da fiye da masana’antun sarrafa taki guda 90 da ke aiki, abin da ya ba ƙasar damar zama mafi girma wajen samar da taki a yankin Saharar Afirka tare da samar da ayyukan yi a gwamnatin da ta rungumi wadata ƙasa da abinci da muhimmanci.
A cewar shugaba Tinubu, tsare-tsaren da aka aiwatar ƙarƙashin Shirin Samar da Taki na Shugaban Ƙasa wanda yanzu aka sake fasalta shi a ƙarƙashin Ma’aikatar Kuɗi na nuna ƙudirin gwamnatin sa na mayar da wadatar abinci a matsayin babban ginshiƙi mai muhimmanci a ajandar gwamnatinsa.
A cewar Tinubu, gwamnatinsa ta bayar da fiifiko wajen tallafawa manoma, ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, rage dogaro da shigo da kaya daga aasashen waje da kuma gina tsarin noma mai ɗorewa wanda zai iya galaba kan matsalolin da ba ka iya tasowa.
Ya ce ya lura cewa tangarɗar da ake samu a fannin samar da kayayyaki a duniya, hauhawar farashin kayan haɗa taki da rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya na haifar da babbar barazana ga yawan amfanin gona da kuma farashin abinci a duniya bakiɗaya.
Ya ce ta hanyar Shirin Taki na Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Ma’aikatar Kuɗi gwamnati ta ƙarfafa tsarin saye da samar da kayayyaki, ta tabbatar da samuwar muhimman sinadaran taki, tare da ƙulla yarjejeniyar samar da kayayyaki da inganta daidaituwa a dukkan matakan samar da taki. A cewarsa hakan ya taimaka wajen kare masana’antun sarrafa taki na cikin gida daga illolin tangarɗar kasuwannin duniya.
Haka ma ya kuma bayyana cewar gabanin shiga damina an riga an tanadi fiye da ton 449,000 na kayan haɗa taki wanda ya yi daidai da buhuna kusan miliyan tara, yayin da jiragen ruwa guda goma ɗauke da kayan taki suka sauke kaya ko kuma suke kan hanyar zuwa ƙasar.
A yayin da gwamnati ke nata ƙoƙarin, wasu manoman na da ra’ayin ya wajaba gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen tallafawa manoma cikin lokaci musamman samar da kayan noma kamar taki, iraruwa da magungunan kashe ƙwari. Hasalima shirin samar da taki a farashi mai sauƙi yana taimaka wajen rage nauyin da ke kan manoma, musamman a wannan lokaci na tsadar kayayyaki.
Ƙungiyoyin manoma da ƙungiyoyin sa-kai da dama sun shiga sahun bayar da gudunmawa ta hanyar wayar da kai da kuma horar da manoma kan yadda za su kare kan su da gonakin su ga ƙalubalen da ke iya tasowa.
Duk da haka masana da manoma na gargaɗin cewa har yanzu akwai buƙatar ƙara tashi tsaye haiƙan musamman wajen tabbatar da cikakken tsaro a yankunan da abin ya fi ƙamari tare da jaddada cewa ba za a iya samun cikakkiyar nasarar noma ba sai an magance matsalar tsaro bakiɗaya.
A kwanan nan ne dai ƴan bindiga suka kai hari ƙauyen Kawel da ke ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Plateau a ƙarshen makon da ya gabata a inda suka kashe aƙalla manoma 20 zuwa 21 tare da jikkata wasu da dama. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun afkawa al’ummar yankin ne a ranar Lahadi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa yawancin waɗanda aka kashe manoma ne da ke zaune a ƙauyen, yayin da gwamnatin jihar ta umarci hukumomin agaji da na ba da tallafin gaggawa su taimakawa iyalan waɗanda abin ya shafa.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci- gaba da nuna damuwa kan matsalolin tsaro a wasu sassan Jihar Plateau, inda hare-haren kan al’ummomin karkara ke ci- gaba da jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
A yankunan Arewa, ƴan ta’adda na amfani da barazana da hare-hare kai tsaye domin hana manoma zuwa gonakinsu ta yadda sau da da dama suke kai farmaki a kan manoma a hanyarsu ta zuwa gona ko ma a cikin gonakin su, lamarin da ke sa mutane tsoron fita bakiɗaya. Tsoratarwar ta haifar da raguwar yawan manoman da ke iya fita noma, musamman a ƙauyukan da suka fi fama da matsalar tsaro.
Wani salo da ya ƙara ta’azzara matsalar shi ne tilastawa manoma biyan abin da ake kira “harajin gona.” Domin kuwa ƴan ta’adda na karɓar kuɗi ko kaso daga amfanin gona kafin su bar manoma su yi noma cikin kwanciyar hankali. Rahotanni sun tabbatar da cewar duk manoman da suka saɓawa umurnin su na iya fuskantar hari, garkuwa da manoman, satar amfanin gona ko ƙone gonakin.
Ɗaya daga cikin ƙalubalen da manoman ke fuskanta baya ga karɓar haraji, ƴan ta’adda na shiga gonaki su lalata amfanin gona ko su kwashe abin da aka noma. A wasu lokuta ma suna sace kayan aikin noma kamar injina, dabbobin noma da taki wanda hakan na jefa manoma cikin asara mai yawa, tare da rage musu ƙwarin guiwar ci-gaba da noma a kakar damina.
A bisa ga waɗannan matsaloli, manoma da dama sun bar gonakinsu sun koma sansanonin ƴan gudun hijira ko garuruwan da ke da wadataccen tsaro. Ƙauracewa noma da manoma ke yi na haifar da ƙarancin abinci a kasuwanni da kuma hauhawar farashi. Haka kuma barazana ce ga wadata ƙasa da abinci musamman a yankunan da suka dogara da noma a matsayin hanyar rayuwa.
Malam Lawal Abdullahi, manomi ne daga Zamfara wanda ya bayyana cewar “A gaskiya muna cikin fargaba sosai saboda hare-haren ƴan ta’adda, amma duk da haka dole ne mu fita gona domin neman abinci. Akwai ƙalubale sosai don haka muna fatar gwamnati za ta ƙara tsaurara tsaro domin mu samu damar noma cikin kwanciyar hankali.”
Shi kuwa Jaɓɓi Mamman a Tangaza a Sakkwato ya bayyana cewar “Ƙalubalen tsaro ya shafi harkar noma sosai, amma ba mu da wani zaɓi face mu ci- gaba. Mun rungumi sabbin hanyoyin noma da kuma haɗin kai tsakanin manoma domin rage haɗari. Abin da muke nema shi ne kariya daga gwamnati da kuma tallafi domin mu samu ingantaccen amfanin gona a wannan damina.”
Bugu da ƙari a wannan watan ne aka samu sabon rahoton yadda ƴan bindiga suka tilastawa mazauna ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon- Birni da ke jihar Sakkwato biyan kuɗaɗen sabon haraji domin tsira da rayukan su gabanin ba su damar zuwa gonakin su.
Majiyoyi daga yankin a gabascin Sakkwato sun bayyana cewa ɓarayin dajin sun bayar da wa’adin kwanaki uku tare da gargaɗin manoma da su guji zuwa gonakinsu har sai sun biya kuɗin da suka buƙata.
Lamarin ya biyo bayan shigowar daminar bana wanda hakan babban ƙalubale ne kuma babbar barazana ce ga noma wadataccen abinci a yankin wanda al’ummarsa suka bayyana cewar ƴan bindigar sun yi alwashin kisa ko sace duk waɗanda suka saɓawa umurnin su a yayin wa’adin.
Garuruwan da lamarin ya shafa sune; Garin- Faji, Cina Barka, Zululu, Ɗan- Gari, Garin- Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin- Ganga, Ɗan- Kware, Garje, Dogon -Faru, Son- Allah, Garin- Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin- Labo, Zango, Kaifin- Aska, Tsauna -Dogo, Tudun- Wada, Rambaɗawa, Ga- Itace, Nasarawa da Garin Idi.
Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya bayyana cewar umarnin ya haifar da tsoro a tsakanin manoma da ke shirin fara noman bana yana cewar sun ce duk wanda aka kama yana noma, ko dai a kashe shi ko a sace shi, kuma ba zai samu ƴanci ba sai ya biya kuɗin fansa na naira 500,000. Ya ce tuni suka fara tattara kuɗaɗe domin biyan harajin.
Wani mazaunin ƙauyen Zululu wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa ranar Juma’a ne lokacin da ya ji labarin wannan umarni.
Ya bayyana cewa ƴan bindigar sun umarci mazauna yankin da su dakatar da duk wasu ayyukan noma na tsawon kwanaki uku har sai ƙauyukan da abin ya shafa sun biya harajin da ake ƙaƙaba masu.
A cewarsu, jami’an tsaro na ƙwace dabbobinsu, suna jaddada cewa ba za a yi wani aikin noma ba har sai an biya harajin da aka ƙaƙaba masu tare da cewar suna tsammanin sarakunan gargajiya da malaman addini za su haɗu su tattauna da ɓarayin dajin domin sanin adadin kuɗin da kowane ƙauye zai biya.
Ya ce “Muna biyan kuɗi kafin mu fara noma, sannan wani lokaci bayan kowane watanni biyu ko uku sai su sake zuwa. Ko bayan mun biya yanzu, za su iya dawowa bayan kusan watanni uku su ce babu wanda zai girbi gero har sai an sake biyan wani haraji.”
“Yawanci suna neman tsakanin naira miliyan 4 zuwa 6 daga kowace al’umma. Mazauna ƙauyuka na bayar da gudummawa gwargwadon ƙarfinsu. Wasu gidaje na biyan naira 1,500 ko 2,000, yayin da a wasu ƙauyuka manoma kan bayar da har naira 5,000 kowannensu, gwargwadon yawan jama’a.”
A yayin da yake magana kan lamarin, kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Sakkwato, Ahmad Rufa’i ya bayyana cewar rundunar ba ta da ko wace irin masaniya kan lamarin. Ya ce mutanen da abin ya shafa ba su cika kai rahoton irin waɗannan matsalolin ga hukumomin tsaro ba.














