Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗan- Fodiyo wanda ya yi gwagwarmayar jihadiin kafa Daular Usmaniyya a 1804, fitaccen malamin Addini, nagartaccen shugaba ne abin koyi, marubucin dubban littaffai a Harsunan Larabci, Fulfulde da Hausa, jagoran yaƙar mulkin danniya da zalunci da tabbatar da mulkin gaskiya da adalci; a shekaru sama da 200 bayan ya yi bankwana da duniya ɗimbin jama’a na ci-gaba da tururuwar ziyarar Hubbarensa da ke Sakkwato.
Hubbaren Shehu Ɗan- Fodiyo da ke Sakkwato babban gidan tarihi ne na addini da ɗaruruwan al’ummar Musulmi suka fi ziyarta domin ganin makwancin Ɗan- Fodiyo wanda ya jagoranci jihadi tare da assasa Cibiyar Daular Usmaniyya.
Tarihi ya tabbatar da cewar gidan da a yanzu yake a matsayin Hubbaren Shehu nan ne ainihin gidan Miujaddadi Shehu Ɗan- Fodiyo a duniyar zamaninsa gabanin ya karɓi kiran mahallaccinsa a rayuwar da ya yi daga 1754 zuwa 1817 a ƙarni na 19.
Ɗan sa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello (1781-1837) shine ya mayar da gidan Shehu a matsayin Hubbaren Shehu. Daga baya gidan ya koma muhallin da aka bizne matansa, ƴaƴansa da manyan sahabbansa da aminansa da ƴan uwansa na jini tare da waliyyai da salihan bayi waɗanda ya yi gwagwarmayar jihadiin kafa Daular Musulunci da su.
Haka ma a Hubbare akwaii Sarakunan Musulunci ɗaya bayan ɗaya har guda takwas da ke kwance a ciki. Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 18, Dakta Ibrahim Dasuki ɗan Halliru ɗan Bara’u ɗan Mujaddadi Ɗan- Fodiyo shi ne na baya- bayan nan da aka rufe kusa da kakansa a 2016.
Tattakin LEADERSHIP Hausa a Hubbare da shiga ciki bayan wuce zauren farko kai tsaye bayan tafiya kaɗan za a ci karo ne da wani gini da ake kira “Jangirde” in da nan ne Makarantar Shehu take wadda yake karantar da Almajiran da ke zuwa ɗaukar karatu a wajensa.
Sai dai duk da gyare-gyaren da aka yi wa Hubbare a shakarun baya, ta na ci gaba da adana tsohon salo da tsarin ginin tarihi, wanda ke nuna asali da martabar da yake da ita tun shekaru aru- aru da dama da suka gabata zuwa yau.
Hubbare na a ƙarƙashin jagorancin Mai Buɗe Hubbare da ke sa idon ganin an bi ƙa’idojin ziyara ba tare da aiwatar da abubuwan da ba daidai ba. Bugu da ƙari Hubbare na a ƙarƙashin kulawar Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
Kabarin Shehu Ɗan- Fodiyo yana a cikin wani madaidaicin ɗaki da aka zagaye tare da ƙawata shi da ƙyalle ruwan shuɗi ɗauke da rubutun larabci, hasalima makwancin Miujaddadi nan ne ainihin ɗakin matarsa Hauwa’u mahaifiyar Sarkin Musulmi, Muhammadu Bello.
Ɗakin da kabarin Miujaddadi yake yana haɗe ne da na ƴaƴansa biyu wato Hassan da Sambo waɗanda suka bi bayansa kwanaki 40 bayan rasuwarsa. Sai dai yadda a ka zagaye kabarin, ya mamaye ɗakin sosai ta yadda mutane ƙalilan ne ke iya shiga, haka ma babu sararin da za a iya ɗaukar hoton kabarin baki ɗaya.
Sarakunan Musulunci da suka shugabanci Daular Usmaniyya da ke kwance a Hubbare sun haɗa da; Sarkin Muslulmi Ahmadu Rufa’i da Sarkin Musulmi Muhammadu Mai- Turare da Sarkin Musulmi Attahiru ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Babba da Sarkin Musulmi Hassan Ɗan Mu’azu da Sarkin Musulmi Abubakar Siddik III har zuwa kan Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo da Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki. Bakiɗaya Sarakunan Musulunci takwas ne kabarinsu yake a Hubbaren daga cikin Sarakuna 19.
Haka ma doka ce mata ba su shiga cikin ɗakin da Mudaddadi yake. Sai dai su kan leƙa ta kofa da taga. Masu ziyara a kabarin Shehu kan yi addu’oin musamman a yayin ziyarar. Haka ma akwai mabarata da dama da ke zaune a bakin ɗakin suna zaman jiran a ba su domin albarkar Shehu.
Ummarunmu Alkammu shi ne babban Sahibin Shehu wanda littaffan tarihi suka bayyana cewar kabarinsa yana a Zomo a Birnin Fulɓe, to amma bisa ga wasu dlilai a na ziyarar kabarinsa a Hubbare wanda a ka zagaye daga wajen ɗakin Shehu a kusa da ƙafafuwan Mujaddadi.
Kabarin Sarkin Musulmi Macciɗo da na Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki an keɓe su ne a waje ɗaya a sashen mata. Daga inda suke za a doshi wani ɗaki na musamman da a ka keɓe wanda a cikinsa ne kabarin matan Shehu huɗu suke a kwance wato Hauwa’u da Shaturu da Gabɗo da kuma Jinnu.
Duk dai a Hubbaren a jere a waje ɗaya akwai kabarin Sarkin Yaƙin Shehu, Aliyu Jeɗo wanda kuma jikan Shehu ne da kabarin Nana Asma’u ɗiyar Shehu da A’ishatu ƴar Ummarunmu Alkammu wadda ita ce matar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.
Haka ma a wajen akwai kabarin Muhammadu Muɗagel, ɗan Alkanmu da kabarin Mai- Hillani da na Limamin Shehu wato Liman Alu. Kabari biyu da ke a wajen an bayyana cewar ba a san masu su ba waɗanda tarihi ya kasa tantance ko waɗanne bayin Allah ne ke kwance a ciki.
Bugu da ƙari akwai ɗakin Hauwa’u matar Mujaddadi wanda cikinsa an zagaye wani waje wanda a ka yi alamar daidai inda Mujaddadi Ɗanfodiyo ke kwantawa. Haka ma a ciki mai ziyara zai ga wani Shantali wanda Shehu Ɗan Fodiyo ke shan ruwa da shi. A yanzu haka kuma ya zama al’ada ga masu ziyara waɗanda kan zuba ruwa a shantalin domin su sha su kuma shafa a jiki domin neman tubarraki a bisa ga yardar su.
Duka a Hubbaren ta sarakuna akwai Marafan Sakkwato Umaru Ali Shinkafi wanda ke auren ƴar Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, da Aishatu ƴar Sa Ahmadu Bello da Sarkin Sudan, Shehu Malami. Haka ma Sarkin Inyamuran Sakkwato, Dakta Muhammad Nweke wanda shine likitan Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ya samu makwanci a Hubbare.
Malam Abdullahi shine Mai Buɗe Hubbare tare da kula da ita ya kuma bayyana cewar ba za a iya bayyana adadin mutanen da ke kawo ziyara kullum a Hubbaren ba. “Ba za a iya ƙayyade masu ziyara a kullum ba domin ko a yanzu ka na ganin ɗimbin mutane ne ke ta shige da fice. Amma a lokacin Sallah Babba da lokacin Mauludi ne lokutan da dubban jama’a suka fi ziyarar Hubbare.”
Ya kuma bayyana cewar a kowace rana Hubbaren a buɗe take daga sanyin safiya zuwa goshin magriba. Sai dai ya ce a ranar Alhamis wadda ita ce babbar ranar ziyara, Hubbaren a buɗe take har zuwa ƙarfe 10 na dare, saboda yawaitar masu ziyara. Don haka an fi ziyara a ranakun Alhamis da Jumaa’.
Ziyarar a Hubbaren ta nuna duk wanda ya rasu a dalilin ziyara shi kansa a kan yi masa kabari a cikin Hubbare. Akwai da yawa waɗanda suka yi hatsarin mota suka rasu a hanyarsu ta zuwa Hubbare waɗanda a yanzu haka a nan aka rufe su a ciki.
Wakilinmu ya labarto cewar duk da yawaitar al’ummar da ke kai ziyara a Hubbare; Fulani ne suka fi yawan tururuwar kai ziyara. Da yawa daga ciki sukan fito ne daga Jihohin Adamawa da Bauchi da Gombe da Katsina da Kano da Kwara da sauransu.
A kan dalilin da yasa Fulani suka fi yawaitar ziyarar Hubbare, Mai Buɗe Hubbare ya bayyana cewa ba mamaki saboda Shehu ya fito daga ƙabilarsu ne amma kuma ɗimbin mutane daga wasu ƙabilun suna kawo ziyara sosai.
Hassan Abdurrahman yana ɗaya daga cikin waɗanda LEADERSHIP Hausa ta ci karo da su sun kawo ziyara a Hubbaren daga Jihar Bauchi ya kuma bayyana dalilisu na kawo ziyara “Muna zuwa Hubbare ne domin neman tubarraki wajen Shehu kuma muna jin daɗi da farin ciki idan muka ziyarci Shehu. A wannan ziyarar mun zo mu 10, wannan ziyara ita ce ta uku da muka kawo muna kuma roƙon Allah yadda muka zo nan lafiya ya kai mu Makka lafiya.”
Shi kuwa Buba Sani wanda ya jagoranci wata tawaga daga Gombe ya bayyana cewar abu ne mai matuƙar muhimmanci ziyarar Hubbare da suke yi a kowace shekara. Ya bayyana cewar “Wannan ita ce ziyara ta 9 da muka kawo a Hubbaren Shehu, kuma muna zuwa ne domin neman albarkar Shehu. A kowace shekara muna zuwa kuma Allah ne yake rufa mana asiri shi yasa muke kawo wannan muhimmiyar ziyarar.”
Da yawan dai masu ziyara a Hubbaren Shehu bayan kammala ziyara tare da yin addu’oin da suka wajaba, su kan zarce kai taye zuwa Rijiyar Shehu da ke a Sakkwato da Wurno da Gwandu. Haka ma masu ziyarar kan je gulbin Ƙofar Kware wanda suke da imanin cewar bayan sun ziyarci Hubbare suka kuma ziyarci gulbin suka yi wanka tare da ɗibar ciyawar bakin gulbin suka ba dabbobinsu, to su kan samu warakar da suke nema tare da ƙaruwar arzikin dabbobi bisa ga imanin su.
Ziyara a Hubbaren Shehu kai tsaye za ta tabbatarwa mai ziyara yadda katafaren wurin tarihin ke buƙatar cikakken gyara domin ɗaga darajarsa. Hasalima idan aka yi la’akari da irin tasiri, martaba da muhimmancin da gidan yake da shi a tarihin Musulunci a Afrika ta Yamma, ya kamata Majalisar Sarkin Musulmi da gwamnatin Sakkwato su bashi kulawar musamman tare da aiwatar da aikin gyara mai inganci domin kare gidan mai daɗaɗɗen tarihi domin amfanin al’ummomi masu tasowa.
Haka kuma, duk da ƙoƙarin da masu kula da Hubbare ke yi, akwai buƙatar ƙara inganta tsaftar muhalli a kodayaushe da kuma kyautata yanayin da baƙi ke tararwa. Samar da wuraren zama, allunan bayanai na tarihi da kuma ƙawata muhallin zai ƙara ɗaukaka darajar wurin tare da jawo hankalin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje.
Bugu da ƙari, Hubbaren Shehu ba kawai wurin ziyara ba ne, alama ce ta tarihin jihadi, ilimi da shugabanci nagari a ƙasar Hausa. Saboda haka, kiyaye shi da bunƙasa shi ya kamata ya zama wani muhimmin ɓangare na manufofin Masarauta da gwamnati na adana kayan tarihi da bunƙasa yawon buɗe ido, domin irin waɗannan wurare na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma wayar da kan al’umma game da tarihin su.














