ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

by El-Zaharadeen Umar
3 hours ago
Garkuwa

A daidai lokacin da hukumar jarabawar kammala sakandire ta WASSCE ke cigaba da gudana a sassan Nijeriya, tsoro da rashin tabbas na kara zama barazana a zukatan dalibai da malamai wanda ke neman maida hannun agogo baya.

Malamai da iyaye da suka tattauna da Leadership sun bayyana fargabar su game da matsalar tsaro da ke kokarin shafar akalla dalibai 1.9 wanda yanzu haka suke rubuta jarabawar kammala sakandire a fiye da cibiyoyi 24,000 a faddin Nijeriya

An fara jarabawar kammala sakandire ta WASSCE a ranar 21 ga watan Afrilu da gwaje-gwaje inda ake sa ran kammalawa a ranar 19 ga watan Yuli 2026

ADVERTISEMENT

Wannan damuwa na zuwa ne a daidai lokacin da aka sace dalibai a makarantun jihar Barno da Oyo wanda yanzu haka dalibai da malamai da dama suna hannun ‘yan bindiga fiye da kwanaki ashirin

Lamarin dai kamar yadda masu ruwa da tsaki da suka tattauna da wakilin mu, sun bayyana cewa hakan ya jefa tsoro da rashin tabbas a wuraren koyo da koyarwa, sannan ya jefa wata sabuwar tambaya akan makomar dalibai dangane da yiyuwar maida hankali da jarabawar a irin wannan yanayi.

LABARAI MASU NASABA

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

Shugabannin kungiyar dalibai ta kasa NANS sun bayyana wannan lamari da cewa, ci gaba da kai irin wadannan hare-hare a makarantun na neman wuce tunanin wasu al’ummomi da abin ya shafa

A cewar su, ko daliban da ke rubuta wannan jarabawa a wuraren da babu matsalar tsaro na iya shiga yanayin firgici akan makomar makarantun su, inda za su iya tunanin kila nan gaba makarantun su na iya fuskantar irin wannan matsala.

Haka kuma sun kara da cewa duk da wannan jarabawa na cigaba da gudana, kiran su ga gwamnatin tarayya da na jihohi shi ne a dauki tsauraran matakai akan makarantu, sannan su yi kokarin kubutar da wadanda suke tsare a hannun ‘yan bindiga. Kazalika su maido da kyakkyawan fatan da ake da shi akan ilimi domin yara masu tasowa.

A daidai lokacin da ake hada wannan rahoto, manyan makarantu guda biyu a jihohin Barno da kuma Oyo sun hadu da hare-haren ‘yan bindiga inda yanzu haka dalibai da malamai suna can a tsare hannun masu garkuwa da mutane

A jihar Borno ana zargin ‘yan Boko Haram da Kungiyar ISWAP ne suka kai hari, makarantar jika ka dawo ta gwamnati da wata firamare da kusa da Mussa a karamar hukumar Askira/Uba a ranar 16 watan Mayu, 2026

Sai dai a lokacin kai wannan hari, an kwamishe kimanin dalibai 42, inda har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wanda aka bayyana cewa an kukutar da shi a gwamnatacce, wanda haka ke nuni da cewa sun kwashe kwanaki 19 ke nan a tsare hannun ‘yan bindiga.

Bayan faruwar wannan al’amari gwamnatin jihar Barno ta ba da umarnin a rufe tare da canzawa makarantun da abin ya shafa wuri ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma ‘yan bindigar sun kai wani hari a garin Ogbomoso, a ranar 15 watan Mayu, 2026 a wata makarantar al’umma da ke Ahoro-Esinele Yawota da kuma firamare ta L.A da ke karamar hukumar Orilire ta jihar Oyo

A wannan hari dai an kwashe mutane 46 da suka hada da dalibai 39 da kuma Malamai guda 7. Sannan babu wata sanarwa daga gwamnati na kubutar da ko da mutum daya, wanda hakan ke nuni da cewa sun kwashe kwanaki 20 suna tsare hannun ‘yan bindiga.

Dalibai da Malaman da har yanzu suna tsare a hannun ‘yan bindiga sun hada da na makarantar jika ka dawo ta gwamnatin da ke Mussa, Askira/Uba, da kuma firamaren da ke kusa da su, inda yanzu dalibai 42 sun yi batan dabo a jihar Borno, sai kuma dalibai 39 da malamai 7 na Ahoro-Esinele a karamar hukumar Orilire ta jihar Oyo

Shima da yake tsokaci game da wannan lamari na rashin tsaro, duk da cigaba da jarabawar WAEC da gudana, babban sakataren kungiyar Malamai na Kasa reshen jihar Ogun, Samson Oyelere ya yi gargadin cewa lamarin na iya yin tasiri matuka ga daliban da ke zauna jarabawa

A bashi bangaren sakataren musamman na kungiyar Malamai ta kasa reshen jihar Dakta Samson Oyelere ya yi gargadin cewa yanayin na ina shafar kokarin da kwazon daliban da ke zauna jarabawa a halin yanzu

“Na yi imani cewa, wannan al’amari zai yi tasiri sosai ga daliban da suke cikin wannan jarabawa, saboda an jefa tsoro da firgici a zukatan su, wanda hakan zai shafi kokarin su a jarabawar. Sannan dalibai da ke rubuta jarabawar WAEC kuma suna fuskantar barazanar masu garkuwa da mutane hakan na iya sanya mu su karayar zuciya dangane da abinda ke gaba su” inji shi

Ibeabuchi Oyelere ya yi gargadin cewa cigaba da sace dalibai tare da yin garkuwa da su na iya haifar da mummunan sakamako a sha’anin koyo da koyarwa a Nijeriya.

“Wannan lamari na iya haifar da gagarumar matsalar rashin zuwa makaranta, ilimi zai samu koma baya ta hanyar sauyawa ilmi wurin zaman da ake gani da aminci. Sannan iyaye za su cigaba da barin ‘ya ‘yan su a gida musamman mata, wanda Nijeriya na iya rasa al’ummar da zai yi alfahari da ita anan gaba.’ inji shi

Ya ce domin a maido da amince a makarantu, ya roki gwamnati da ta kara tura jami’an tsaro a makarantu tare da kafa wata tawagar ko kwana, sannan ayi saurin hukunta wadanda ke da hannu a wannan sace-sacen dalibai daga karshe a samar da wani yanayi da taimakawa daliban da abin ya shafa

“Aminci zai dawo lokacin da dalibai suka samu kansu a yanayi na tsaro, ba wai lokacin da ake daukar masu alkawarin ba su tsaro ba” inji shi

Da yake magana dangane da wannan al’amari, shugaban kungiyar dalibai na kasa NANS Kwamared Akinteye Afeez, ya jarabawa zata cigaba da gudana, amma gwamnati a dukkanin matakai dole a dauki matakin samar da tsaro a makarantu.

Haka kuma ya yi gargadin cewa cigaba da sace dalibai zai naunana fatan da ake da shi a kan sha’anin ilimi tare sanyaya gwiwar koyo a yankunan karkara.

A cewar sa, daliban Nijeriya sun fara dawowa rakiyar wannan tsari, ya ce yanzu al’umma sun fi amincewa su je makarantun cikin birni da suke da tsaro, a maimakon su tsaya a garuruwan su na karkara inda anan ne talaka ke iya samun damar yin karatu.

“Ya kamata gwamnati ta samar da shingayen jami’an tsaro a kusa da makarantu domin karfafa tsaro da bada kariya tun bayan faruwar wannan lamari ” inji shi

Ya kara da cewa shugabannin kungiyar dalibai ta NANS yanzu haka suna Jihar Oyo kuma suna aiki domin ganin an sako wadanda dalibai da aka yi garkuwa da su.

A nata bangaren, ma’ajin kungiyar dalibai ta NANS Kwamared Asma’u Idris ta bayyana tsoro akan yanayin tsaron dalibai da ke zauna jarabawa kammala sakandire ta WASSCE a halin yanzu.

“Batun gaskiya shi ne, bana tunanin daliban mu suna cikin yanayi na tsaro, saboda haka akwai bukatar a samar da kyakkyawar tsaro, sannan gwamnati ta dauki batun rayuwar wadannan yaran da ke zauna jarabawa da matukar mahimmanci” inji ta

Asma’u Idris ta ce satar dalibai ta dade tana ci masu tuwo a kwarya, wanda take gargadin cewa harkar ilimi a Nijeriya na iya shiga wani hali idan har ba a dauki mataki ba.

“Yanzu malamai ba su da kwarin gwiwar koyarwa a makarantu, sannan wasu na can suna neman wata damar a kasashen waje, ilmin mu zai iya shiga wani hali mai tsanani idan haka ta cigaba da faruwa” inji ta

Wata Uwa mai suna Theresa Christopher wanda diyar ke zauna jarabawar kammala sakandire ta WASSCE a makarantar gwamnatin tarayya da ke Gboko a jihar Binuwai ta ce dole ne gwamnati ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an dawo da aminci a tsakanin dalibai ta hanyar samar da tsaro tare hukunta masu kai hare-hare a makarantu

“Yanzu ko daliban da ba sa fuskantar barazanar tsaro a makarantun su, sun fara jin tsoro da kuma sakawa a ran su cewa wani abu na iya faruwa da su, wanda hakan zai iya shafar kokarin su a lokacin yin wannan jarabawa.” Inji ta

A cewar ta, magance matsalar tsaron da ta addabi makarantu shi ne abinda ya kamata gwamnatin tarayya ta baiwa fifiko a halin yanzu.

“Idan har da gaske muke yi a kan sha’anin ilimi a Nijeriya, dole ne a ajiye komai gefe guda a tunkari matsalar tsaron nan” inji ta

Shima Sanata a kungiyar dalibai ta NANS Kwamared Moses Ibeabuchi ya bayyana cewa rashin tsaro na iya shafar kokarin dalibai a yanayin da ake ciki.

“Idan dalibai suka san cewa ana kai hare-hare a makarantun su a bangarori daban-daban na kasar nan, to za su iya zama cikin fargaba ko da acikin dakin jarabawa ne, sannan da yawa daga cikin su, za su sanya shakku game da tsaron lafiyar su. Wanda wannan tsoron kawai na iya shafar kokarin su wajen jarabawa. ” Inji shi

Ibeabuchi ya yi gargadin cewa barin matsalar tsaro ta tsawaita na iya haifar da sanyaya gwiwar Malamai daga shiga ajujuwa wanda hakan na iya nakasa harkar ilimi a Nijeriya.

Haka kuma ya roki gwamnati da ta ba da tabbacin tsaro a kan rayuka da dukiyoyi sannan ta kara shigo da masana da kuma kwararu a kan sha’anin tsaro domin baiwa makarantu da wuraren kwanan dalibai kariya a fadin Nijeriya

“Ina da tabbaci a kan jami’an tsaron mu. Abin da kawai suke neman shi ne, tallafi da sauran fasalin tafiyar da lamarin tare da karfafa gwiwa domin su tunkari wannan babban kalubale” inji shi

Wata da ta ce a sakaya sunan ta ta gargadi gwamnatin Nijeriya da ta yi taka tsantsan a kan sha’anin masu garkuwa da mutane kada ta dauki batun da wasa ko kadan

Lokacin da ‘yan Boko Haram suka fara kai hare-hare, sun fada a fili cewa kudirin su shi ne, wargaza ilimin boko da turawan yamma suka shigo da shi, su maye gurbin sa da ilimin addinin Musulunci.

Ya ce yanzu babu abinda suke yi sai kai hare-hare a makarantu inda suka jefa tsoro a zukatan al’umma da dalibai da kuma Malamai. Yanzu ba sun kama hanyar cimma wannan manufa ta su ba, ta hanyar  sanyaya gwiwar dalibai daga zuwa makaranta?

“Dole ne gwamnatin tarayya ta dauki yaki da ‘yan ta’adda da mahimmancin gaske fiye da komi, ba don wani abu ba, sai don ceto matasa manyan gobe” inji ta

Garkuwa
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Matsalar Tsaro: Manoma Sun Koma Gonakinsu A Katsina – Dikko Radda
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Batun Kammala Aikin Gina Gidaje 250 Na “Renewed Hope” Ya Bar Baya Da Kura A Jihar Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Yusuf Buhari Ya Halarci Zaɓen Fidda Gwani Na Sanatan Shiyyar Daura

MASU ALAKA

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri
Rahotonni

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

June 13, 2026
Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
Rahotonni

Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

June 13, 2026
Me Kashim Imam Ke Yi A Yanzu?
Rahotonni

Me Kashim Imam Ke Yi A Yanzu?

June 8, 2026
Next Post
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

June 13, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026
Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

June 13, 2026
An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

June 13, 2026
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

June 13, 2026
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutun Biyu Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Adamawa

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.