ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

by Sani Anwar
3 weeks ago
Arewa

Gwamnonin yankin Arewa-maso-yamma, sun fara yunkurin aiwatar da tsare-tsare da nufin magance talauci, ta hanyar fadada shirye-shiryen kare al’umma da sabbin hanyoyin samar da kudi a fadin jihohi bakwai na yankin.

An kaddamar da shirin ne, a ranar Talata a birnin Kano, a yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu na manyan tsare-tsare kan rage radadin talauci, wanda kungiyar Gwamnonin Arewa-maso-yamma tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya suka shirya tare da tallafin Tarayyar Turai (EU) da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

Da take jawabi a wajen bude taron, Darakta-Janar ta Sakatariyar Kungiyar Gwamnonin Arewa-maso-yamma, Maryam Yahaya ta ce; tattaunawar ta nuna wani muhimmin mataki na fassara alkawuran yankin zuwa ayyuka na musamman da za su inganta rayuwar miliyoyin mutane.

ADVERTISEMENT

Ta yi nuni da cewa, duk da dimbin arziki na yawan al’umma da tattalin arzikin da yankin yake da shi, yankin Arewa-maso-yamma, na ci gaba da fuskantar kalubalen ci gaba mai yawan gaske, wadanda suka hada da talauci, rashin lafiya, rashin tsaro, lalurar yanayi da dimbin yaran da ba sa zuwa makaranta.

A cewarta, kalubalen sun zarce iyakokin jihohin, sannan kuma suna bukatar hadin kai a yankin.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

“Arewa-maso-yamma, yanki ne da yake da babbar dama, amma kuma muna ci gaba da fuskantar manyan kalubale na ci gaba. Wannan tattaunawa ta kasance wani bangare na tsarin aiwatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban Arewa-maso-yamma, cika alkawuran yankin ta hanyar yin ayyuka masu amfani da kuma tsarin kare lafiyar al’umma, samar da kudade ta hanyar hadin gwiwar zuba jari a ci gaban mutane, “in ji ta.

Ta kara da cewa, taron zai yi aiki tare da gwamnatoci, abokan ci gaba, kungiyoyi masu zaman kansu, cibiyoyi masu zaman kansu da kuma shugabannin gargajiya, domin gano hanyoyin samar da kudade masu dorewa da za su iya rage radadin talauci idan aka sanya a sikeli.

Ita ma a nata jawabin, shugabar ci gaban al’umma ta kungiyar Tarayyar Turai, Dr. Leila Amor, ta ce; Tarayyar Turai (EU) na alfahari da goyon bayan wannan shiri, inda ta bayyana rage radadin talauci a matsayin daya daga cikin kalubalen gaggawa da yankin Arewa-maso-yamma da Nijeriya baki-daya ke bukata.

Har ila yau, ta jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa a yankin, tare da lura da cewa; talauci da rashin tsaro, sun yi matukar katse iyakokin jihar.

“Tarayyar Turai, ta bayar da cikakken goyon bayan kokarin karfafa tsarin kariyar zamantakewa da kuma inganta sakamakon ci gaban al’umma a fadin Arewa-maso-yamma. Talauci bai tsaya a kan iyakoki kadai ba, hadin gwiwar yanki na iya magance shi yadda ya kamata, “in ji Amor.

Mataimakin wakilin UNICEF a Nijeriya, Dr. Rownak Khan, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin da ake yi na magance fatara a yankin.

Ya ce, Jihohin Arewa-maso-yamma bakwai, na da kusan mutum miliyan 60, sannan kuma suna fuskantar munanan matsaloli wadanda suka shafi jin dadi da walwalar yara a kasar.

A cewarsa, mace-macen mata masu juna biyu a yankin, ya zarce 1,000 a duk cikin 100,000 na wadanda suka haihu, mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar, ya kai kashi 140 cikin 1,000 na masu rai, yayin da kusan kashi 60 cikin 100 na yara ke fama da matsalolin daban-daban.

Khan ya ba da shawarar bullo da wani shiri na amfanin yara na duniya, yana mai bayyana shi a matsayin tabbatacciyar dabarar rage talaucin yara, inganta shigar makarantu da kuma karfafa karfin iyalai.

Da yake bayyana bude taron a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Garo, ya ce; ya kamata a dubi batun kare al’umma a matsayin wani shiri na zuba jari, wajen bunkasa jarin al’umma da ci gaban tattalin arziki, maimakon a matsayin shirin jin dadin jama’a.

Ya ce, Kano ta riga ta samar da dokar kare hakkin jama’a tare da kafa Cibiyar Kare Jama’a, don daidaita ayyukan da aka yi niyya ga masu rauni.

Garo ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa, tattaunawar ta haifar da manufofi da tsare-tsare masu amfani da za su inganta rayuwar al’umma a fadin yankin Arewa-maso-yamma.

Arewa
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Gwamnati Ta Amince Da Inganta Cibiyar Kula Da Saran Maciji A Gwambe
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Hukumar NDLEA Ta Lalata Sama Da Tan 12 Na Miyagun Ƙwayoyi A Kano
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
Rahotonni

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

June 26, 2026
Noma
Rahotonni

Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

June 26, 2026
Next Post
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

LABARAI MASU NASABA

Dakarun Tsaron Teku Na Sin Na Ci Gaba Da Sintirin Wanzar Da Doka A Yankunan Ruwa Na Gabashin Tsibirin Taiwan

Dakarun Tsaron Teku Na Sin Na Ci Gaba Da Sintirin Wanzar Da Doka A Yankunan Ruwa Na Gabashin Tsibirin Taiwan

July 4, 2026
Wasu Matasa Amurkawa Sun Ziyarci Sin Don Kara Fahimtar Kasar

Wasu Matasa Amurkawa Sun Ziyarci Sin Don Kara Fahimtar Kasar

July 4, 2026
Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

July 4, 2026
CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

July 4, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

July 4, 2026
Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

July 4, 2026
Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

July 4, 2026
Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

July 4, 2026
Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

July 4, 2026
Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

July 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.