A yau Laraba, Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ta zanta tare da shan shayi da kuma ziyartar wani karamin baje kolin kayayyakin sana’ar hannu tare da Entissar El-Sisi, maidakin shugaban kasar Masar, Abdel-Fattah El-Sisi.
Peng ta tattauna cikin yanayi na zumunta tare da Entissar game da dangantakar abota tsakanin Sin da Masar da kuma mu’amalar al’ummomin kasashen biyu.
Peng ta bayyana cewa, Masar tana da dogon tarihi da kuma gadon al’adu masu zurfi, inda ta yi nuni da cewa, kayan tarihi masu ban sha’awa da aka baje kolinsu, sun bayyana irin hikima da kuma basirar tsara kayan ado ta musamman da al’ummar Masar ke da ita.
Peng ta kuma ce, Sin da Masar suna da kamanceceniya da dama a fannin al’adu, tana mai bayyana fatan cewa masu sana’o’in fasaha daga kasashen biyu, za su karfafa mu’amala da hadin gwiwa domin bai wa sana’o’in gargajiya damar ci gaba da haskakawa tare da sabon kuzari ta hanyar gado da kuma koyon juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














