Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na sake fasalin Hukumar Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima NYSC. Wannan shawarra ta haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin ƴan Nijeriya, inda wasu ke ganin alfanun haka yayin da wasu ke ganin akasin hakan, wasu kuma na ganin ya kamata a yi takatsantsan. Ga ra’ayoyin kamar yadda Wakilanmu, Shehu Yahaya, Sani Anwar da Muhammad Baƙir suka kawo mana.
Sanata Shehu Sani, daga Kaduna
Sake fasalin Hukumar NYSC abu ne mai kyau, amma ya kamata Darakta Janar (DG), na hukumar ya ci gaba da kasancewa soja, ba ɗan siyasa ko masani daga jami’a ba. A kowane hali, bai kamata a soke horon soja da ake bai wa masu yi wa ƙasa hidima ba.
Ƙasar da ke fuskantar irin waɗannan manyan ƙalubale na tsaro, tana buƙatar irin wannan horo a yanzu fiye da kowane irin lokaci.
Mairo Muhammad Mudi, Suleja
Sake fasalin Hukumar NYSC, ba abu ne da ba shi da kyau ba, idan har zai iya magance matsalolin da suka daɗe suna damun shirin, ba tare da lalata manufarsa ta asali ba.
A cewar bayanan da gwamnati ta fitar, daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su akwai:
Mayar da shugabancin gudanarwar Hukumar NYSC ga farar hula, maimakon soja. Ƙara lokacin sansanin horaswa daga makwanni uku zuwa shida.
Bai wa masu yi wa ƙasa hidima horo na koyar da sana’o’i, fasahar zamani da kuma kasuwanci.
Ƙara matakan tsaro da amfani da fasahar zamani wajen tsarin kira da tura masu hidima.
Idan aka aiwatar da waɗannan gyare-gyare yadda ya kamata, za su iya:
Samar wa matasa ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun aikin yi ko fara kasuwanci.
Inganta tsaron masu bautar ƙasa. Sanya NYSC ta dace da buƙatun ƙarni na yanzu.
Sai dai, akwai wasu abubuwan da ya kamata gwamnati ta kula da su: Kada a bar manufar haɗa kan al’ummar Nijeriya ta dusashe.
A tabbatar an samar da isassun kuɗi da kayan aiki kafin a ƙara tsawon lokacin horo.
A ci gaba da kare lafiyar masu yi wa ƙasa hidima, musamman a wuraren da ake fama da matsalolin tsaro.
A saurari ra’ayoyin tsofaffin masu bautar ƙasa, jami’o’i da masu ruwa da tsaki, yayin aiwatar da gyaran.
A taƙaice, ba sunan “gyara” ne yake da muhimmanci ba, illar yadda za a aiwatar da shi. Idan gyaran zai ƙara wa matasa ilimi, ƙwarewa, tsaro da damar dogaro da kai, zai zama abin matuƙar so, amma idan zai ƙara musu wahala ba tare da wata fa’ida mai ma’ana ba, to zai buƙaci a sake duba wasu daga cikin matakan.
Musa Nuhu, daga Kano
Batu na gaskiya shi ne, gwamnati na son lalata wannan hukuma ce, dalili kuwa farar hula ba zu iya jajircewa, kamar yadda soja yake jajircewa ba.
Haka nan, wannan wuri na masu horar da ƴan bautar ƙasa (NYSC Camp), zai zama tamkar wani filin wasa ne, ba wurin bayar da horo ba.
Usama Yusuf Muhammad, daga Bauchi
Wannan batu na canza fasalin Hukuman NYSC, ba abu ne mai kyau ba magana ta gaskiya, mussaman canza Darakta Janar daga soja ya koma farar hula. Mutane da dama na zuwa bautar ƙasa ne, saboda sojoji ne ke tsaye a kai, amma idan ya koma hannun farar hula, wallahi za a fara kawo wa mutane sakifiket ne har gida, saboda wasu za su yi amfani da sanayya, cin hanci da rashawa zai yi yawa sosai a wajen.
Sannan kuma, lokacin da aka sa na kasancewa a wajen bautar ƙasar (Camp), ya yi yawa, ni a ganina da an gyara abin ne an rage yawan watannin ana haɗa kuɗaɗen, ana ba su kawai a matsayin jari, su kama sana’a.
Sani Bello, daga Zaria
Eh to! Gaskiya ina ganin wannan sabon tsari na NYSC ɗin, idan aka tabbatar da shi, zai fi tsohon tsarin da muke kai yanzu. Dalili kuwa shi ne, an fitar da rukunin horaswa har guda goma sha ɗaya, wanda zai yi daidai da karatun mutum a jami’a.
Ta wannan hanyar ɗalibai za su samu gogewa, basira da kuma shiri wa ayyukan da za su tunkara bayan bautar ƙasa. Saɓanin tsarin da muke kai yanzu, wanda ya fi maida hankali wajen horon soji da koyarwa a ajujuwa.
Daga ƙarshe, babban abin da yake damun ƙasarmu shi ne, cin hanci, rashawa da rashin gaskiya. Idan aka tabbatar da wannan tsari ba tare da waɗannan abubuwa ba, tabbas ƴan ƙasa za su samu horaswar da suke buƙata.
Mahadi Isa Waziri, daga Zaria.
Wannan tsari ne mai kyau da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi, saboda an shigo da wasu tsare-tsare, waɗanda za su taimaka wa matasa, musamman waɗanda ba sa cikin tsarin NYSC.
Sannan, tsawaita lokacin zama a Kam, zai bayar da dama masu bautar ƙasa su koyi abubuwa sosai fiye da da. Alal misali, lokacin da na yi bautar ƙasa, a cikin sati ɗaya aka ba mu horo a kan kiwon kaji, wanda idan dai ana so mutum ya koya sosai, lallai wannan bai wadatar ba.
Sannan ba na goyon bayan canza Khaki na NYSC, da janye horon soja da ake bayarwa, sai dai ya kamata a bar shi a matsayin zaɓi ga wanda yake so ya yi.
Haka zalika, tsarin rashin tura mutane yankuna da suke fama da rashin tsaro abin a yaba ne. Saboda hakan shi ne yake hana wasu zama wuraren da aka tura su.
Mohammed Sani Jibril, daga Kaduna
A matsayina na ɗalibi mai yi wa ƙasa hidima a Jihar Kaduna, ba na goyon bayan duk wani sabon tsari da zai sauya abubuwan da aka saba yi a shirin NYSC tsawon shekaru.
Dalili kuwa shi ne, wannan tsari ya daɗe yana wakiltar NYSC, kuma da zarar an ga mutum cikin kayan nan ana gane ɗan bautar ƙasa ne.
Daga cikin abubuwan da za a sauya, akwai batun sauya kayan, wanda hakan ba zai kawo wani alfanu ga shirin ba. Saboda haka, ba na ganin akwai amfani a irin wannan sauyi.
Jafaru Maitama Yakubu, daga Kaduna
Shugaban ƙungiyar ƴan jarida musulmi ta ƙasa ya ce, na farko ina da ra’ayin mayar da shugabancin Hukumar NYSC, ƙarƙashin soja, saboda a tabbatar da tarayya a tsakanin matasa.
Haka kuma, ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen koyar da masu bautar ƙasa sana’o’i, tare da ba su jari na fara yin kasuwanci, bayan sun kammala hidimarsu.
“Gwamnatin tarayya ta tabbatar cewa, duk wani sauyin da za a aiwatar, zai mayar da hankali wajen inganta rayuwar matasa, samar musu da ƙwarewar sana’o’i da kuma ƙarfafa musu gwiwar dogaro da kai, bayan kammala bautar ƙasa”.
A cewarsa, “Ya kamata gwamnati, ta bai wa kowane mai bautar ƙasa jarin naira miliyan ɗaya, bayan an koya masa sana’a, wanda hakan zai fi amfanarsu. Hakan zai bai wa matashi ilimi da sana’a a lokaci guda, amma sauya kayan sawa, ba shi da wani amfani a ganina ko sauya shugabancin hukumar, duk ba zai taimaka da komai ba,” in ji shi.
Malam Mohammed Aminu Ibrahim, daga Anchau Jihar Kaduna
Magidanci mai ƴaƴan da suka kammala bautar ƙasa, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗaɗen alawus-alawus da ake bai wa masu yi wa ƙasa hidima, saboda tsadar rayuwar da ake ciki.
“Ya kamata a ƙara kuɗin alawus-alawus zuwa aƙalla naira 100,000, domin kuwa 77 da ake biya a yanzu ba su wadatar ba, musamman ga waɗanda ke bautar ƙasa a jihohi kamar Legas, Ribas da Abuja, inda tsadar rayuwa ta fi yawa,” in ji shi.
“Kazalika, ya dace a ci gaba da amfani da kayan da aka saba amfani da su, domin girmama tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), wanda aka kafa shirin na NYSC a zamaninsa.













