ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

by Sagir Abubakar
44 minutes ago
NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata tsohuwa mai shekara 67, ƴar Nijeriya kuma ƴar Birtaniya, Misis Mary Barek, bisa zargin yunƙurin safarar kilogram 13 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin ɓawon ayaba na jabu ta Filin Jirgin Saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Hukumar ta bayyana cewa an kama wacce ake zargin, wacce ke aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya a Birtaniya, a sashen masu fita na Terminal 2 na filin jirgin, yayin da take ƙoƙarin hawa jirgin Ɓirgin Atlantic zuwa birnin Landan.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce bincike mai zurfi da aka yi wa jakunkunanta ya kai ga gano manyan ƙunshi 31 na hodar iblis (cocaine) da aka shirya su kamar gungun ayaba, tare da haɗa su da sauran kayan abinci.

ADVERTISEMENT

Babafemi ya ce: “Binciken da aka yi wa jakunkunanta ya kai ga gano manyan ƙunshi 31 na hodar iblis da aka shirya su kamar gungun ayaba, waɗanda nauyinsu ya kai kilogram 13.”

Ya ƙara da cewa a bayanin da ta bayar, tsohuwar ta amsa cewa hodar iblisin da aka kama mallakinta ce.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

Hakazalika, Babafemi ya sanar da kama wani ɗalibi mai shekara 45 mai digirin digirgir (PhD) a Jami’ar Putra ta Malaysia, Nwabueze Feliɗ Onyeka, bisa zargin ƙoƙarin fitar da hodar iblis da aka ɓoye a cikin kwali na abin sha Orijin Bitters zuwa Kuala Lumpur.

Ya ce an kama Onyeka a ƙaramar hukumar Ekwusigo ta Jihar Anambra a ranar 29 ga Yuni, bayan bincike ya gano shi a matsayin shugaban wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Babafemi ya bayyana cewa jami’an NDLEA sun fara kama ƙunshi 36 na hodar iblis masu nauyin kilogram 5.80, waɗanda aka ɓoye a cikin bangon kwali tara na abin shan ganye da aka shirya jigilar su zuwa Malaysia.

Ya ce a farkon binciken an kama mutane huɗu a Legas, ciki har da wakilin jigilar kaya Alalade Taiwo Azeez, direban da ya ɗauko kayan Ndem Ogbonna Kelechi, wani ɗan kasuwa a Kasuwar ASPANDA da ke Trade Fair Compleɗ, Okeke Tochukwu Chimezie, da kuma Igwilo Chidi Henry, wanda ake zargin shi ne ya samar da kwalayen da aka ɓoye miyagun ƙwayoyin a ciki.

Babafemi ya ce: “Ƙoƙarin binciken ya haifar da gano Nwabueze, wanda ke ɓoye a ƙauyensa na Aziora, Ozubulu, a Jihar Anambra, a matsayin shugaban ƙungiyar.”

A Jihar Taraba, NDLEA ta ce jami’anta sun kama wani mutum mai shekaru 30, Daniel Harrison Ugwuoke, a kan hanyar Zaki-Biam da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a ranar 4 ga Yuli.

Hukumar ta ce an kwato kwantena 43,980 na Tramadol, waɗanda aka ɓoye a cikin tankunan mai guda biyu da aka ƙera musamman domin ɓoye miyagun ƙwayoyin.

A Jihar Kaduna, jami’an NDLEA sun kuma kama Boniface Agu mai shekaru 65 da Monday Nwaeze mai shekaru 50 a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Gwantu ranar 2 ga Yuli, inda aka ƙwato kilogram 1.7 na methamphetamine.

A Jihar Ebonyi, an kama wani mutum mai shekaru 65, Francis Ifara Eja, da kilogram 231.7 na skunk a Ikwo ranar 4 ga Yuli.

Haka kuma, a Jihar Filato, an kama wani mutum mai shekaru 75, Alhaji Babani, da kilogram 15 na skunk a Kurgwi, Ƙaramar Hukumar Ƙua’an Pan, ranar 3 ga Yuli.

A Jihar Gombe, NDLEA ta ce ta kama mutane biyu, Dahiru Mohammed mai shekaru 65 da Isiya Lawan mai shekaru 36, a ranar 1 ga Yuli, tare da bulo 587 na tabar wiwi (Cannabis satiɓa) masu nauyin kilogram 556 a ƙauyen Kuri, Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba.

Baya ga ayyukan kama masu laifi, NDLEA ta ce ofisoshinta a faɗin ƙasar sun ci gaba da gudanar da shirin Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi (WADA) ta hanyar wayar da kai a makarantu, wuraren aiki, cibiyoyin ibada da al’ummomi.

Babafemi ya ce an gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a a Makarantar Sakandaren Ƴan Mata ta Abagana a Jihar Anambra, Goɓernment Technical College da ke Obe a Jihar Enugu, Adeola Odutola College da ke Ijebu Ode a Jihar Ogun, da kuma FCE Staff Demonstration School da ke Kabuga a Jihar Kano, da sauran wurare.

Da yake yabawa jami’an da suka gudanar da waɗannan ayyuka, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa ofisoshin MMIA, Taraba, Kaduna, Ebonyi, Filato da Gombe saboda nasarar kama masu laifi da ƙwato miyagun ƙwayoyi.

A cewar Babafemi, Marwa ya ce ya yaba da yadda jami’an suka haɗa aikin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma shirye-shiryen wayar da kan jama’a na WADA, tare da ƙarfafa su da sauran jami’an hukumar a faɗin ƙasar su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukansu.

NDLEA
Sagir Abubakar
+ postsBio
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Gwamnan Katsina Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Cibiyar Gyaran Motoci Mai Amfani Da Hasken Rana
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Gwamnatin Jihar Katsina Na Shirin Samar Da Tsarin Kula Da Masu Cutar Daji
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Hukumar RUWASSA Ta Kudiri Aniyar Samar Da Ruwa A Fadin Jihar Katsina
  • Sagir Abubakar
    https://hausa.leadership.ng/author/sagir-abubakar/
    Barayin Shanu Sun Kashe DPO A Karamar Hukumar Rimi Ta Jihar Katsina

MASU ALAKA

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi
Tsaro

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

July 10, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026
CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

July 10, 2026
Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.