ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin gina gidaje 20,000 a duk shekara, yayin da ta ce kusan gidaje 15,000 na kan matakai daban-daban na kammalawa a faɗin ƙasar nan. Haka kuma, gwamnatin ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Raya Ƙasa ta Jamus (GIZ) domin hanzarta samar da gidaje masu araha da bunƙasa birane a Nijeriya.

Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin wata ganawa da tawagar Jamus ƙarƙashin jagorancin Dakta Karin Jansen, Shugabar Haɗin Gwiwa ta Ofishin Jakadancin Jamus a Nijeriya. A cewarsa, haɗin gwiwar na daga cikin ƙoƙarin aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman wajen samar da gidaje masu araha, da inganta ci gaban birane da gina ababen more rayuwa masu ɗorewa.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da neman hanyoyin rage ƙarancin gidaje a Nijeriya ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyi da ƙasashen waje. Ya bayyana cewa ma’aikatar na kammala shirye-shiryen Tsarin Gidajen Jama’a (Social Housing Scheme), wanda zai ba da damar samar da gidaje masu araha a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar. Shirin zai fi mayar da hankali kan masu ƙaramin ƙarfi, ciki har da malamai, ma’aikatan lafiya, masu buƙata ta musamman, matasa masu iyali da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje masu neman gidaje masu sauƙin samu.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, Darma ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta fara aikin sauya fasalin aƙalla manyan unguwanni uku marasa ingantaccen tsari kafin ƙarshen shekarar 2026, a matsayin wani ɓangare na shirin raya birane.

A nata ɓangaren, Dakta Karin Jansen ta ce Jamus a shirye take ta faɗaɗa haɗin gwiwa da Nijeriya a fannonin raya birane masu ɗorewa, gine-ginen da ke rage amfani da makamashi da kuma ababen more rayuwa masu jure sauyin yanayi. Ita ma Sakatariyar Dindindin ta ma’aikatar, Dakta Shuaib Belgore, ta bayyana cewa wannan haɗin gwuiwa zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin gidaje da inganta rayuwar al’ummar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.