ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
Aure

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi bayyana hotunan ma’aurata kafin aure da bayan aure.

A wannan zamanin kai ya waye wanda a wajen wasu abu ne wanda ya zama dole, da zarar za a yi aure sai an bayyanawa duniya hotunan aure tun kan a yi auren da kuma bayan auren. Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Shin mene ne riba ko kuma alfano game da hakan?, Ko akwai wata matsala da za ta iya afkuwa sanadiyyar hakan ko da bayan aure, wanda su ma’auratan ba su hango shi ba?”

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

ADVERTISEMENT

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

Rayuwa ce ta zo da canji, yanzu da dama wani lokacin kana bayyanawa baki yakan tarwatsa abu, wasu kuma suna ganewa sai su bata abu, ya dai danganta. To, wasu sukan boye saboda faruwar matsaloli, wasu kuma ba sa boyewa ra’ayinsu ne. Amma ni ina ganin boyewar shi ne alfano saboda zamanin da ake ciki yanzu, mace sai ta iya zuwa ta kashe maka aure ko kuma ta bibiyi mijin da soyayya ko makamancin haka.

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki

Sunana Sarauniya Nasmah, daga Jihar Zamfara:

Ina ganin a nawa fahimtar yin hoto kafin aure abu ne da zamani ya zo da shi, ya zama kamar cikin al’adun bukukuwa, kuma mutane tun a lokacin suke sanin hidimar biki fa ta taho. Babu wata riba ko rashin riba a ciki, hidimar kawai ce take zuwa da shi, ya dangata dai da ra’ayin wanda zai yi. Ita matsala ai ba a iya hangota ta aure ko kafin aure, ko an yi wadannan hotuna ko ba a yi ba sai hakan ya faru, amma idan har an kaddara ta silar hoton za a samu matsala wannan daban ne. Shawara dai da zan bayar ita ce a yi taka-tsantsan wajen yin hoton, kar a kaucewa al’adunmu na hausawa, duk da shi ma hoton ba al’ada ba ne, amma dai akalla in an yi hoton a tuna martabar al’adarmu .

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Mutane suna jin dadi, suna nuna farin ciki, kuma suna samun albarka da adduo’i daga abokai da dangi, wasu suna amfani da shi don tallata kansu ko neman kasuwa. Matsalolin da za su iya afkuwa sun hada da  iddiba, kishi, hassada daga mutane, ko kuma sharri tare da baki ko a ce kambun-baka. Bayan aure kuma idan aure ya lalace, wadannan hotuna na iya zama damuwa ga bangarorin biyu haka zalika tsaron sirri ma yana  iya raguwa. Shawarar da zan iya bayarwa ita ce a  daure a ajiye wasu hotuna na sirri ga iyali kawai, a dauki hotuna masu mutunci ba tsirara ba, wanda babu nuna tsiraici a ciki a tuntubi mazaje/mata kafin a dora komai, aure sirri ne, ba komai ya dace a nuna wa duniya ba.

Sunana Fatima Nura kila, daga Jihar Jigawa:

A gaskiya ba shi da wani amfani, kawai dai yanzu matasa Maza da Mata sun dorawa kansu rayuwar karya, shi ya sa ake hakan a ce mijinta wanene ko ai matar wane ce, wadda kuma mun kauce koyar war addinin Musulunci. Tabbas yana haifar wa, domin shi ya sa yanzu aure baya albarka saboda mutane sun gama tofa albarkacin bakinsu, tun da kowa da kalar bakinsa. Ya kamata su Maza su rika kishin matansu, domin koyarwar addinin Musulunci, ka kare iyalinka, haka ita ma mace ta guji yada hotunansu tun da sirrin su ne.

Sunana Lawan Ismail (Lisary), Rano, daga Jihar Kano:

Babu riba kuma Babu Alfanu. Akwai matsaloli da yawa, domin a wannan zamanin kadan da sharrin mutanen ciki ka ga hoton wani dana amaryar, ko ki ga hoton angon da wata. Shawarata ita ce mutane su daina wannan banzar al’adar domin duk wani mai kishin iyalinsa ba zai so ana yada wadannan hotunan ba.

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, daga Jihar Kano:

Wayewa ce, amma a rashin wayewa ka gama tallan matarka duk duniya ta sani. Babu riba sai faduwa wani bakinsa zai yi fatan alkhairi wani kuma zai ta binku da bita da kulli. Wani lokacin matsaloli na yawan aikuwa wani in ya kyalla ido zai ji shi fa duk duniya ita wannan matar taka yake so, daga nan zai yi duk mai yiwuwa ya ga ya raba wannan auren domin cikewar nufinsa. Babbar shawara a kiyaye a yi abin cikin tsari musulunci duk da abin kala-kala ne wani in ki ka gani zata za ki yi ma ba ‘ya’yan musulmi bane, Allah dai ya shirya mana zuri’a ya dawo damu hanyar Aurenmu na iyaye da kakanni yafi dadi walahi.

Sunana Princess Fatima Mazadu, Gomben Nijeriya:

Yana bawa dangi, abokai da masoya damar taya ma’auratan murna. Yana zama wata hanya ta sanar da jama’a game da bikin aure. Yana samar da abubuwan tunawa da za a iya adanawa a matsayin tarihin rayuwa. Wasu na amfani da shi wajen nuna godiya ga wadanda suka tallafa musu a shirye-shiryen aure. Yawaita bayyana rayuwar aure ga jama’a na iya jawo tsokaci ko suka daga mutane. Wasu na iya nuna hassada ko mugun fata, wanda zai iya haifar da damuwa ga ma’auratan. Hotunan da aka wallafa a intanet na iya ci gaba da yawo har bayan shekaru da dama ba tare da ikon gogewa gabadaya ba. Wani lokacin ma’aurata kan fuskanci matsin lamba na nuna cewa komai yana tafiya daidai, alhali suna da kalubalen rayuwar aure kamar kowa. Su tabbatar cewa abin da suke wallafawa ya dace da addininsu, al’adunsu da ka’idodin mutunci. Ma’aurata su amince tare kafin a yada hotuna ko bayanai da suka shafe su. Su fi mayar da hankali kan gina kyakkyawar rayuwar aure fiye da neman yabo ko karbuwa daga mutane a intanet. Su tuna cewa nasarar aure tana ta’allaka ne a fahimtar juna, hakuri da amana, ba yawan hotunan da aka wallafa ba. Yada hotunan aure ba laifi ba ne a wurare da dama idan an yi shi cikin mutunci da hankali. Amma yana da kyau ma’aurata su daidaita tsakanin bayyana farin cikinsu ga jama’a da kuma kare sirrin rayuwar aurensu, domin sirri na daga cikin ginshikan zaman lafiya da dorewar aure.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, karamar hukumar Dala, Jihar Kano:

Wasu na hakan a matsayin hanya ta sanar da dangi da abokai farincikinsu ko kuma adana tarihin wani muhimmin mataki a rayuwa. Hakan na iya kara wa mutane farinciki da samun fatan alheri daga jama’a. Sai dai kuma ba kowa ne yake ganin ya zama dole ba, domin aure ba ya samun kima ta yawan hotunan da aka yada, abin da ke nuna kimar aure ita ce kyakkyawar zamantakewa da fahimtar juna tsakanin ma’aurata. A gefe guda, akwai matsalolin da ka iya tasowa idan ba a yi taka-tsantsan ba, kamar kutsen masu mugun nufi cikin rayuwar ma’aurata, yawan tsokaci daga jama’a, ko kuma yada bayanan sirri fiye da kima. Wasu lokuta ma mutane kan fuskanci matsin lamba saboda kokarin nuna rayuwa mai armashi a kafafen sada zumunta. Shawarar da zan ba wa masu shirin aure ita ce su kasance masu taka-tsantsan,

Aure
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
Taskira

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

June 13, 2026
Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
Taskira

Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki

May 29, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Taskira

Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

May 24, 2026
Next Post
Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza

LABARAI MASU NASABA

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomi 10

June 27, 2026
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Aka Cimma Tsakanin Amurka Da Iran

Iran Ta Jaddada Cewa Ba Ta Da Wani Shiri Na Bada Damar Binciken Wuraren Nukiliyarta

June 27, 2026
Ribar Manyan Kamfanonin Sin Ta Karu Da Kashi 18.8% Cikin Watanni Biyar Na Farkon Bana

Ribar Manyan Kamfanonin Sin Ta Karu Da Kashi 18.8% Cikin Watanni Biyar Na Farkon Bana

June 27, 2026
Yaushe Za A Gane Kungiyar Da Za Ta Lashe Gasar Premier?

An Raba Jadawalin Gasar Premier Ta Ingila Ta Kakar Wasan 2026/2027

June 27, 2026
Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

June 27, 2026
Kofin Duniya

Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya

June 27, 2026
Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

Wakilin Sin: Kar A Bari Sabon Nau’in Ra’ayin Nuna Karfin Soja Ya Haifar Da Karin Tasiri

June 27, 2026
Manoma Sun Nemi Tinubu Ya Kara Yawan Tallafin Noma 

Ko Shirin Da Gwamnatin Jihar Katsina Ke Yi Wa Manoma Zai  Amfane Su A wannan Daminar?

June 27, 2026
CDC Ta Afirka Ta Yaba Da Goyon Bayan Da Sin Ta Bayar Da Hadin Gwiwa Mai Karfi Wajen Yaki Da Ebola

CDC Ta Afirka Ta Yaba Da Goyon Bayan Da Sin Ta Bayar Da Hadin Gwiwa Mai Karfi Wajen Yaki Da Ebola

June 27, 2026
Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

June 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.