ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago

Ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka a wasansa na ƙarshe na kofin duniya a ranar Litinin yayin da burinsa na lashe kyautar mafi girma ya ƙare da rashin nasara a hannun ƙasar Sifaniya da ci 1-0.

Kyaftin ɗin na Portugal mai shekaru 41 kuma ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa na duniya ya ce yanzu zai tafi ya yi tunanin abin da zai biyo baya. Ronaldo Ya lashe duk wata kyauta da ƴan ƙwallo ke da burin lashewa ya kuma buga wasa a manyan ƙungiyoyin Turai. Amma baya ga Cristiano Ronaldo akwai fitattun ƴan wasa da suka buga a matakin duniya suka kuma lashe kyaututtuka da dama amma suka kasa lashe kofin duniya musamman ganin yadda aka yi waje da tawagogin ƙasashensu daga gasar bana, kuma ana kyautata zaton cewa ba za su sake dawowa su fafata a gasar nan da shekara huɗu masu zuwa ba. Wasu daga cikinsu ma sun riga sun sanar da cewa wannan ita ce gasar kofin duniyarsu ta ƙarshe.

Ronaldo – Portugal

ADVERTISEMENT

A ranar Litinin bayan da Portugal ta sha kashi a hannun Spain da ci 1-0. Tauraron ɗan wasa Cristiano Ronaldo na Portugal yana da shekaru 21 lokacin da ya fara buga gasar cin kofin duniya. Wannan gasar ta kasance ta shida – wani abin da shi da Lionel Messi na Argentina kaɗai suka iya yin hakan.

Yayin da yake da shekaru 41, Ronaldo shi ne ɗan wasa na biyu mafi tsufa a gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar. Duk da haka, ya zura ƙwallaye uku – wanda ya tabbatar da cewa har yanzu yana da rawar da yake iya takawa a fagen ƙwallon ƙafa na duniya. Kawo yanzu Ronaldo ya koma gida ba tare da ya lashe kambun gasar cin kofin duniya ba.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Fitaccen ɗan wasan na Portugal ya shafe shekaru sama da ashirin, yana hanƙoron lashe kofi ɗaya da ya bayyana a fili a matsayin babban burinsa. Bayan gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022, Ronaldo ya yarda cewa daga kyautar da ya fi so a ƙwallon ƙafa ita ce “burinsa mafi girma.” Sai dai wannan mafarkin ya ƙare yanzu, kuma bisa ga dukkan alamu kambun gasar cin kofin duniya ya kuɓuce wa ɗaya daga cikin manyan fitattun ƴan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, wanda za a daɗe ba a manta rawar da ya

taka wajen nishadantar da masoya ƙwallon ƙafa ba.

Neymar – Brazil

Burin Neymar na lashe gasar kofin duniya ya ƙare cikin baƙin ciki yayin da tauraron na Brazil ya fashe da kuka bayan da Norway ta fitar da zakarun gasar kofin duniya sau biyar a zagaye na ƴan16 a filin wasan New York New Jersey. Hotunan da aka nuna a talabijin sun nuna Neymar yana kuka ba ƙaƙƙautawa bayan kayen da Brazil ta sha da ci 2-1. Wannan hoto ya zame mai tayar da hankali, ba wai kawai saboda Brazil ta fice

daga gasar cin kofin duniya ba, amma saboda wataƙila wannan shi ne lokaci na ƙarshe da za a ga Neymar a babban matakin ƙwallon ƙafa.

Baya ga zama babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil, Neymar ya ci ƙwallo sama da 100 a ƙungiyoyi uku daban-daban: Santos, Barcelona da Paris Saint-Germain. Tsohon ɗan wasan Brazil Romario da Cristiano Ronaldo ne kawai suka cimma irin wannan bajinta a ƙwallon ƙafa ta zamani ta maza, amma Neymar shi ne na farko da ya yi hakan a nahiyoyi uku daban-daban.

Neymar ɗan wasa ne mai matuƙar baiwa inda ya lashe kofunan lig a Spain da Faransa da kuma lashe gasar zakarun Turai ta UEFA a 2015.

Luka Modric – Croatia

Luka Modric da Croatia sun sha kashi a gasar cin kofin duniya ta 2026 a hannun Portugal. Wannan rashin nasarar nan take ta haifar da rashin tabbas game da makomar shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya mai shekara 40.

Amma, kamar yadda ya ambata kafin gasar cin kofin duniya, hakan ya tabbatar da ritayar Luka Modri daga buga wa Croatia wasa, bayan ya tabbatar da matsayinsa na gwarzon ɗan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa wanda ya taimaka wa Real Madrid ta mamaye fagen ƙwallon ƙafa a Turai, kuma ya jagoranci Croatia zuwa ƙololuwar fagen ƙwallon ƙafa na duniya.

Bayan zaman da ya yi a Real Madrid inda ya lashe kyautuka dama da kuma zaman da ya yi a AC Milan a kakar wasa da ta gabata, Modric ya yanke shawarar rataye takalmansa a hukumance.

Modric wanda nan ba da jimawa ba zai cika shekaru 41 ya lashe manyan kofuna da dama a lokacin da yake buga wasa a Real Madrid. Sannan shi ne wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2018 wanda ya karya mamayar da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka yi wa kyautar na tsawon shekaru 10.

Har ila yau, Modric ya lashe gasar zakarun Turai sau shida, kuma ya lashe manyan kofuna 28, wanda ya sanya ya zama ɗan wasa mafi lashe kyautuka da ya taɓa saka rigar Real Madrid.

Riyad Mahrez – Algeria

Shima ɗanwasa Riyad Mahrez ya sanar da yin ritaya daga buga wa Algeria wasa bayan da Algeria ta sha kashi a hannun Switzerland da ci 2-0 a zagayen ƴan 32 na gasar cin kofin duniya ta 2026. Tsohon ɗan wasan na Manchester City ya bayyana cewa ya shafe shekaru 12 yana buga wa ƙasarsa wasa, wanda ya haɗa da lashe gasar kofin nahiyar Afrika (AFCON).

Mahrez ya sanar da hakan ne a lokacin da yake magana da kafar yaɗa labarai ta beIN SPORTS bayan da aka fitar da Algeria daga gasar. Ya ce rashin nasarar da aka samu a gasar cin kofin duniya ya kawo ƙarshen wasansa na ƙasa da ƙasa bayan shafe fiye da shekara 10 yana wakiltar ƙasarsa inda ya buga wasanni 119.

Edin Dzeko – Bosnia

Za a iya cewa yan wasa ƙalilan ne kawai za su iya goga kafaɗa da ɗan wasan Schalke Edin Džeko ta fannin cin ƙwallaye. Ɗan wasan dai ya murmure daga raunin da ya yi fama da shi ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da matsayin ƙasarsa a gasar. Džeko, ɗan wasan Bosnia mafi hazaƙa da yawan zura ƙwallaye, ya shafe shekara 20 yana buga ƙwallo a matakin mafi girma a fagen ƙwallon ƙafa a duniya. Ɗan wasan mai shekaru 40 ya nuna cewa har yanzu yana iya buga wasa a matakin mafi girma. na Dzeko, wanda ya buga wa tawagar ƙasarsa wasa 148, ya buga wasanni bakwai daga cikin takwas da ƙasarsa ta yi a rukunin H na neman gurbin shiga gasar ta bana. ƙwallo 65 da ya ci sun tabbatar da shi a matsayin ginshiƙi a tarihin ƙwallon ƙafa na ƙasarsa.

Ronaldo
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.