ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

by Abubakar Abba
2 months ago
NPA

Gamayyar Kungiyoyin Tabbatar da Sauye-Sauye ta Kasa wato NCTR, sun jinjina wa Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, kan sabbin sauye-sauyen da ya kirkiro da su, a Hukumar, a karkashin shugabancinsa.

A cewarsu, wadannan sauye-sauyen da Dantso ya kirkiro da su a NPA, tuni, kwalliya ta fara biyan kudin Sabulu, a fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar.

Sun yi nuni da cewam nadin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yiwa Dantsoho, a matsayin shugaban NPA bai yi zaben Tunun dare ba, musamman duba da irin kyawawan sauye-sauyen da Dantsoho, ya samar da fannin.

ADVERTISEMENT

Kungiyoyin sun kara da cewa, wadannan sabbin sauye-sauyen, sun kuma kara karfafa gudanar da ayyukan NPA tare da kara karfafawa alummar kasar, guiwa, musamman yadda Dantsoho, ya zamanantar da ayyukan NPA

Babban Daraktan gamayyar kungiyoyin Dakta Richard Ocheje, ya bayyana haka, a cikin sanawar da ya fitar a Abuja, inda kuma ya yabawa  gwamnatin shugaba Tinubu, kan wanzar da tsare-tsaren da suka saita fannin sufurin Jiragen Ruwan kasa, musamman yadda ake ci gaba da zuba jari da kara tabbatar da gasa da kuma kara habaka fannin tattalin arzikin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

A cewar Ocheje, sauye-sauyen wadanda suka karade kowanne bangare, musamman na samar da kayan aiki na zamani ga NPA, sun kara taimaka wa, wajen kara ingnata ayyukan NPA, tare da daga darajar NPA, musamman a yankin Afirka ta Tsakiya

Ya kara da cewa, Hukumar a karkashin shugabancin Dantsoho, ta kirkiro da shiye-shiryen da suka kara bunkasa ayyukanta, musamman duba da yadda suka kara bunkasa kokarin da gwamnatin kasar ke ci gaba da yi, na tabatar da ana yin gaskiya, wajen tafiyar da ayyukan NPA.

“A cikin dan karamin lokaci, NPA a samu nasarar daga kimar ta, musamman a matsayina na Hukumar da ke sanya ido a tafiyar da ayyukan Hukumar,” A Ocheje.

Ya ci gaba da cewa, samar da shirye-shiryen ayyukan zamantar da NPA, sun kara taimaka wa, wajen zuba jari, a fannin.

A cewarsa, yarjejeniyar Fam miliyan 746 na kudin Ingila  da aka rattaba hannu a watan Maris din 2026, ana sa ran, za ta taimaka wa, aikin zamanantar da Tashishin Jiragen Ruwa na Apapa da Tin Can Island, da ke a jihar the Legas.

Kazalika, ya ce, gwamnatin tarayya na shirin kashe dala biliyan daya, a cikin shirin aikin Tashoshin Apapa, Tin Can Island, Kalabar, Warri, Fatakwal  da kuma na Onne.

Ocheje ya kara da cewa, gwamnatin shirin fara yin aikin wasu Tashohin na Badagry, Olokola, Ibom, Bakassi da Bonny, wadanda za su kara taimaka wa, ayyukan na NPA.

Ya kuma yabawa gwamnatin, kan zamantar da ayyukan NPA, musamman kan tsarin NSW, wanda ya ce, hakan ya taimaka, wajen rage jinkirin kawar da kayan da aka yo jigilarsu da kuma kara bunkasa hada-hadar kasuwanci.

Ya kuma bayyana jin dadinsa kan gabatar da kudurin kafa Hukumar Sanya Ido kan fannin tattalin arzikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar wato NPERA da Majalisar kasar ta yi.

A cewarsa, idan aka amince da kafa wannnan Hukumar, musamman ta kasance mai cin gashin kanta, zai taimaka wajen sanya ido na kudin harajin da ake karba a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar da kuma kara ingnata ayyukan NPA.

Kazalika, gunyiyoyin sun bayyana cewa, wanzar da sauyen-sauyen da ake ci gaba da yi a NPA. Za su kara taimaka wa, wajen samar da saukin yin kasuwanci, janyo hankalin masu zuba jari da suransu.

Tuni dai, gwamnatin kasar, ta ayyana fannin kusanci na take a matsayin wani bangare na kara habaka fannin tattalin arzikin kasar.

Tun bayan kafa ma’aikatar ta bunkasa tattalin arzikin Teku a 2023,  gwamnatin kasar ta kirikiro da shirye-shirye da dama, tare da daga darajar kayan aiki da kuma kula da shige da ficen kayan da ake shigowa da zuwa Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.

NPA
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.