ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

by Sulaiman
6 days ago
Kudi

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga KowaKwanan nan, wani dan siyasar Amurka ya gurbata gaskiya game da yanayin cinikin kasar Sin, inda ya ayyana ci gaban Sin a matsayin “barazana”, kuma ya jirkita zabin kasuwa, cewa wai “Sin tana yunkurin neman rarar kudin ciniki fiye da saura”.

Amma gaskiyar lamari ita ce bangaren Sin ba ya neman samun rarar kudin ciniki fiye da saura da gangan, kuma yana adawa da duk wani nau’in matakan haraji na kare kai. Gibin ciniki yana faruwa ne bisa tarin dalilai kamar bukatun kasuwa da takarar kasuwa a duniya.

Yadda Sin ke samun rarar kudin ciniki na nuna cewa, Sin tana da cikakken tsarin masana’antu mai inganci, haka kuma sakamako ne na kwaskwarimar da ake yi a bangaren rarraba ayyuka da tsarin ciniki na duniya. Karuwar cinikin fitar da kayayyaki na Sin ya samo asali ne daga karuwar karfinta ta fannin kirkire-kirkire, kana daga bukatun kasashe na samun ci gaba ba tare da gurbatta muhalli ba da ci gaban masana’antun duniya.

ADVERTISEMENT

A bangaren rarraba fa’idodin ciniki kuwa, rarar kudin ciniki da Sin ta samu na amfanar da mabanbantan bangarori. Alal misali, a shekara ta 2025, kamfanoni masu jarin waje sun ba da gudunmawar kashi 27% na cinikin fitar da kayayyaki zuwa ketare na Sin, kuma yawan kudin fannin ya kai kashi 16% na rarar kudin ciniki da Sin ta samu, kana saurin karuwar rarar kudin ciniki da riba da wadannan kamfanoni suke samu ta fi na kamfanonin cikin gida.Dadin dadawa, ko da yake Sin tana samun rarar kudi a bangaren cinikin fitar da kayayyaki zuwa ketare, a daya bangaren tana yawan kashe kudi a bangaren shigo da hidimomi daga ketare, da amfani da asusun jari da na hada-hadar kudade, kuma rarar kudin ciniki da Sin ke samu a yau da kullum ya kai kusan kashi 3.7% na GDPnta, adadin da kasa da kasa ke ganin ba matsala da shi, kuma ba a gano rashin daidaiton ciniki tsakaninta da sauran kasashe ba.

A cikin shekaru 5 da suka gabata, jimillar kayayyakin da Sin ta shigo daga ketare ta wuce yuan tiriliyan 90, wanda ya nuna cewa Sin ba wai kawai “cibiyar samar da kayayyaki ta duniya” ba ce, har ma “kasuwar duniya” ce. Har ila yau, Sin ta riga ta aiwatar da manufar soke haraji kan kayayyakin da take shigowa daga kasashe 63, kuma jimillar harajin ya ragu zuwa kashi 7.3%. Sin ita ce babbar kasa ta farko a duniya da ta aiwatar da manufar soke haraji kan dukkanin kayayyakin da take shigowa daga dukkan kasashen Afirka da suka kulla huldar diplomasiyya da ita, da kuma dukkan kasashe mafi karancin ci gaba da ke da huldar da ita.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Sakamakon manufar, a watanni Mayu da Yuni na bana kadai, kudin kayayyaki da kasar Sin ta shigo daga kasashen Afirka ya kai dala biliyan 28.5, wanda ya karu da kashi 23.5% bisa na makamancin lokacin bara. Ban da wannan kuma, a rabin farkon wannan shekara, kudin kayayyakin da kasar ta Sin ta shigo daga Nijeriya ya kai biliyan 2.25, wanda ya karu da kashi 81% bisa na makamancin lokacin bara.

Bugu da kari, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE, shi ne bikin baje koli irinsa na farko a duniya wanda ya mayar da hankali kan shigowa da kayayyaki, kuma kawo yanzu an gudanar da shi sau 8 cikin nasara, inda darajar jimillar kwangilolin shigar da kayayyaki Sin da aka cimma ta wuce dala biliyan 580.Tushen gibin ciniki da Amurka ke fuskanta ya samo asali ne daga kanta, ciki har da rashin isasshen kudin ajiya, da koma bayan masana’antu, kana da kayyade fitar da fasahohin zamani zuwa Sin, idan har Amurka ba ta gyara manufofinta, lallai da wuya ta daidaita wannan matsala.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana kwanan nan cewa, “Dole ne Sin da Amurka su hada kai don tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da magance matsaloli ta hanyar tattaunawa bisa daidaito, da mutunta juna da cin moriya tare, su kuma kiyaye kyakkyawan yanayin da suke samu a fannin kasuwanci da tattalin arziki.”Sin ba ta da niyyar neman samun rarar kudin ciniki, kuma ba za ta dakatar da bude kofarta ga ketare ba duk da cewa wasu sun “kafa mata shingaye”.

Daga Afirka zuwa Latin Amurka, daga kudu maso gabashin Asiya zuwa Gabas ta Tsakiya, kasashe da yawa suna tabbatar da cewa yin ciniki da Sin dama ce a maimakon barazana. Samun rarar kudin ciniki ba “laifi” ba ne, cin moriya da samun nasara tare ita ce mafita ga kowa, kuma Sin za ta dage wajen bude kofarta ga ketare a ko da yaushe. (Marubuciya: MINA)

Kudi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • Sulaiman
    Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Yadda Afirka Ke Rungumar Amfani Da Damar Da Sin Ke Samarwa
Ra'ayi Riga

Yadda Afirka Ke Rungumar Amfani Da Damar Da Sin Ke Samarwa

August 28, 2026
Next Post
Auren Gata: Za A Saka Wa Kowace Amarya Kuɗin Sadakinta N200,000 A Asusunta

Gwamna Yusuf Ya Sha Alwashin Daukar Matakin Gaggawa Bayan Hare-Haren ’Yan Bindiga A Kano

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.