Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren ’yan bindiga da aka kai a wasu kananan hukumomi hudu na jihar, inda ya tabbatar wa al’ummomin da lamarin ya shafa cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji, da kuma wasu al’ummomi da ke kusa da Gwarzo.
Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyyarsa da jaje ga wadanda hare-haren suka rutsa da su da iyalansu, yana mai bayyana abubuwan da suka faru a matsayin abin damuwa matuka kuma wanda ba za a amince da shi ba.
Ya tabbatar wa al’ummomin da lamarin ya shafa cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin hana sake afkuwar irin wadannan hare-hare da kuma dawo da kwarin gwiwar jama’a kan tsaro.
Gwamnan ya ce ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi kan aikinsu, tattara bayanan sirri da kuma inganta hanyoyin gaggauta tunkarar duk wata barazana a yankunan da lamarin ya shafa.














