Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya bai wa Folashade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da Ministar Fasaha da Tattalin Arziƙin Masana’antu, Hannatu Musa Musawa, sarautun gargajiya.
An bai wa Tinubu-Ojo, wadda ita ce Iyaloja-Janar ta Legas, sarautar Jakadiyar Ƙasar Hausa, yayin da aka bai wa Musawa sarautar Mairamar Ƙasar Hausa.
An gudanar da bikin cikin armashi a Fadar Sarkin Daura, bayan kammala Hawan Magajiya, wanda aka fi sani da Sallar Gani.
An ba su waɗannan sarauta ne domin karrama irin gudummawar da suke bai wa al’umma, musamman wajen bunƙasa al’adu, tallafa wa mata da kuma ci gaban al’umma.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, da wasu jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi sun halarci bikin.













