Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani III, ya rasu yana da shekaru 84 bayan fama da rashin lafiya a ƙasar Masar.
Wata majiya daga fadar sarkin ta tabbatar wa jaridar Kano Times rasuwar sarkin a ranar Alhamis.
Majiyar ta ce sarkin ya rasu ne a ƙasar Masar.
Ana sa ran fadar sarkin za ta sanar da bayanan jana’izarsa nan ba da jimawa ba.
An haifi Sarkin a ranar 12 ga watan Disamba, 1942, kuma shi ne Sarki na 16 da ya hau gadon Sarautar Gumel.
Kafin ya zama sarki, Sani ya yi fice a fannin ilimi da aikin gwamnati.
Ya yi Difloma a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a a shekarar 1963, sannan ya sake samun Babbar Dufloma a wannan fanni a shekarar 1970 daga Cibiyar Gudanarwa da ke Zariya, wadda yanzu take cikin Jami’ar Ahmadu Bello.
Daga baya ya tafi Jami’ar Ohio da ke Amurka, inda ya karanci Kimiyyar Siyasa da Hulɗar Ƙasashen Duniya, kuma ya kammala karatunsa a shekarar 1978.
Daga shekarar 1978 zuwa 1980, Sarkin ya kasance Kwamishinan Yaɗa Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu a tsohuwar gwamnatin Jihar Kano.
A lokacin da yake Kwamishina, ya taka rawa wajen kafa gidan jaridar Triumph da gidan talabijin na CTV67, wanda yanzu ya koma ARTV.
Ya kuma jagoranci faɗaɗa ayyukan Gidan Rediyon Kano.
Ana sa ran fadar Sarkin za ta ƙara bayani kan jana’izarsa da kuma yadda za a zaɓi wanda zai gaje shi.














