Hukumar kula da ayyukan kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta sanar a yau Talata cewa, an zabi mutane 10 da suka hada da matuka kumbo 8 da masu kula da gwaje-gwaje da kayayyakin aiki 2, domin aikin ‘yan sama jannati na kasar Sin karo na 4.
A cewar hukumar, daya daga cikin masu gwaje-gwaje da gudanar da bincike dan asalin yankin musammam na Hong Kong ne, yayin da dayan kuma ya fito daga yankin musammam na Macao. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp